El Rufai Ya Ragargaji Gwamnatin APC, Ya Fadi Bambancinsa da Ita
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake ragargazar gwamnatin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
- Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatin APC na tunanin cewa duk wanda ya rike mukamin gwamnati yana yin rashin gaskiya
- Tsohon gwamnan ya kalubalanci duk wani wanda yake da shaidar cewa ya taba cin hanci to ya fito fili ya gayawa duniya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya kaddamar da kakkausan suka kan jam’iyya mai mulki ta APC.
Nasir El-Rufai ya zargi jam’iyyar da tunanin cewa duk wanda ya rike mukamin gwamnati ɓarawo ne.

Source: Twitter
Tsohon gwamnan na Kaduna ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a cikin wata hira da tashar Arise News a shirin 'Prime Time' ranar Juma’a, 13 ga watan Fabrairun 2026.
Nasir El-Rufai ya yi zargi kan APC
El-Rufai ya yi zargin cewa gwamnatin da APC ke jagoranta tana cikin matsananciyar damuwa kuma ta lashe takobin rufe bakin duk wanda take gani a matsayin ɗan adawa gabanin zaɓen 2027.
Ya yi iƙirarin cewa hukumomi sun daɗe suna gudanar da bincike a kansa tun watan Yunin 2023, amma har yanzu ba su gano wani laifi da ya aikata ba.
“Wannan gwamnatin tana cikin matsananciyar damuwa kuma ta ƙuduri aniyar ganin bayan kowa. Suna tunanin mu ma ɓarayi ne kamar su lokacin da muke gwamnati."
- Nasir El-Rufai
Ana yi wa El-Rufai bita da kulli
Bugu da kari, El-Rufai ya yi zargin cewa an kama tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnati da kuma tsohon kwamishinan kuɗi na jihar Kaduna, tare da wasu manyan mukarrabansa.
Ya ce an tsare su tare da gurfanar da su a kotu bisa zarge-zargen da ya siffanta da "na banza," yana mai jaddada cewa ba a samar da wata shaida ta cin hanci da rashawa ba.
Tsohon gwamnan ya kuma zargi wanda ya gaje shi, Gwamna Uba Sani, da bayar da dama ko goyon bayan waɗannan matakan da ake ɗauka a kansa.
El-Rufai ya ce bai saci dukiya ba
Yayin da yake tunawa da shekarun da ya yi yana aikin gwamnati tsakanin 1999 zuwa 2007, El-Rufai ya ƙalubalanci duk wani ɗan Najeriya da yake da shaidar rashin gaskiya a kansa da ya fito ya bayyana ta.
“Ina ƙalubalantar kowane ɗan Najeriya da ya fito ya tona mini asiri idan har na taɓa karɓar ko kwabo ɗaya na cin hanci lokacin da nake kan muƙamin gwamnati."
“Ina da tarihin aikin gwamnati na shekaru 16, kuma na kalubalanci kowane ɗan Najeriya da ya yi aiki da ni ko ya san ni da ya fito ya tona mini asiri idan har na taɓa karɓar cin hanci, ko na nemi cin hanci."
"Ko na yi wani abu wanda ya saɓa wa doka yayin gudanar da ayyukana. Na faɗi hakan a gidan talabijin, akwai ƴan Najeriya miliyan 250 su fito su nuna cewa ƙarya nake.”
- Nasir El-Rufai

Source: Twitter
Ya bayar da misali da binciken da aka gudanar a kansa lokacin gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, inda ya ce ba a kai ga samunsa da kowane laifi ba.
“Sun bincike ni sosai kuma ba su gano komai ba. A ƙarshe, an gurfanar da ni a kotu kan zargi guda ɗaya, wai lokacin da nake Ministan Abuja, na ba matata fili guda ɗaya daga cikin filaye 27,000. Kuma sun faɗi a shari’ar. Alƙalin ma ya gargaɗi EFCC da kada su sake yin irin wannan abin.”
- Nasir El-Rufai
El-Rufai ya yi bayani kan yunkurin cafke shi
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi magana kan yunkurin cafke shi da jami'an tsaro suka yi.
Nasir El-Rufai ya bayyana cewa jami'an hukumar DSS ne suka yi yunkurin cafke shi a filin jirgin sama bayan ya dawo Najeriya.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ce ta nemi jami'an na DSS su yi ram da shi daga dawo wa Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


