Abu Ya Girma: An Kira Zaman Gaggawa kan Sanya Ranakun Zaben 2027 a Watan Ramadan
- Majalisar wakilan tarayya ta shirya zaman gaggawa ranar Talata mai zuwa kan ce-ce-ku-cen da ya barke bayan fitar da jadawalin zaben 2027
- A ranar Juma'a, 13 ga watan Fabrairu, 2026, INEC ta sanya ranakun zaben shugaban kasa, gwamnoni da yan Majalisar tarayya da na jihohi
- Sai dai ranakun da INEC ta sanya sun fada ne a cikin watan Azumin Ramadan, lamarin da ya jawo suka daga musulmai masu ibada a lokacin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Wakilai ta Tarayya ta kira zaman gaggawa ranar Talata, 17 ga Fabrairu, domin tattauna batutuwan zaɓe da suka taso bayan fitar da jadawalin babban zaɓen 2027.
Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya sanar a ranar Juma’a cewa za a gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Tarayya ranar 20 ga Fabrairu, 2027.

Source: Facebook
A sanarwar da INEC ta wallafa a Facebook, Farfesa Amupitan ya ce zaɓen gwamnoni da na ‘yan Majalisun Dokokin Jihohi za su gudana ranar 6 ga Maris, 2027.
Sai dai wadannan ranaku da INEC ta zaba za su fado ne a watan azumin Ramadan, lamarin da ya sa Musulman Najeriya suka fara suka da neman a sake duba jadawalin zaben 2027.
Majalisar wakilai ta kira zaman gaggawa
Sakamakon haka, Majalisar wakilai ta kira zaman gaggawa ranar Talata mai zuwa domin tattaunawa kan wannan batu na zabe a lokacin da musulmi ke azumi.
Jaridar Daily Trust ta ce an sanar da ‘yan majalisar zaman gaggawar ta wata takarda da Ofishin Kakakin Majalisa ya fitar a daren Juma’a, inda aka jaddada muhimmancin batun bisa ga kundin tsarin mulki.
A cewar takardar, zaman gaggawar na nuna ƙudirin Majalisar Wakilai na daukar matakin da ya dace cikin hanzari kan batutuwan da ke da tasiri mai zurfi ga tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.
Abubuwan da Majalisa za ta tattauna
Ana sa ran tattaunawar za ta mayar da hankali kan batutuwan doka da suka shafi sanarwar da INEC ta yi game da ranakun zabe, bisa ga nauyin da Kundin Tsarin Mulki ya ɗora wa Majalisar Tarayya.
A wata sanarwa daban da Shugaban Ma’aikatan Kakakin Majalisa, Farfesa Jake Dan-Azumi, ya sanya wa hannu, ta ce yan Majalisar za su sake duba kudirin gyaran dokar zabe.

Source: Facebook
Sanarwar ta bayyana cewa zaman gaggawar zai ba ‘yan majalisa damar janye matsayinsu na baya kan Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe, musamman game da lokacin sanar da ranar zaɓe.
Sanarwar ta ce:
“Hakan ya biyo bayan fitar da jadawalin zaɓen 2027 da INEC ta yi, Kamar yadda aka lura, ranakun zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Tarayya sun zo daidai da watan Ramadan, wanda hakan na iya shafar fitowar jama’a.”
Bashir Ahmad ya ja hankalin INEC
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya lura da matsalar da za a iya samu a zaben 2027 saboda musulmai na azumin Ramadan.

Kara karanta wannan
Kotu ta umarci a kawo malamin Musulunci da ake zargi da hannu a shirin yi wa Tinubu juyin mulki
Bashir Ahmad ya yi gargadin cewa gudanar da zaɓe a irin wannan lokaci da musulmai ke maida hankali wjaen ibada,na iya kawo ƙalubale mai girma.
Ya ce mutane ka iya kauracewa zaben idan har suka fahimci za sus ha wahala saboda ibadar azumi, wacce tana da matukar muhimmanci a rayuwar kowane musulmi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

