Ganduje Ya Tara Malami da 'Yan Siyasar Kano, Ya Gayyaci Aminu Ado Bude Masallaci

Ganduje Ya Tara Malami da 'Yan Siyasar Kano, Ya Gayyaci Aminu Ado Bude Masallaci

  • Tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da sabon masallacin da gidauniyarsa ta gina a jihar Kano
  • Rahotanni sun nuna cewa Abdullahi Ganduje ya gayyaci mai martaba Aminu Ado Bayero buden masallacin da aka yi ranar Juma'a
  • Manyan 'yan siyasa, malamai daga ciki da wajen Kano da sun shaida bude masallacin da aka ba Sheikh Lawal Shuaibu Abubakar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Mai martaba Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero ya halarci bude sabon babban masallacin Juma'a da aka gina a jihar Kano.

Tsohon shugaban jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya halarci bude masallacin da aka ce shi ya gina.

Abdullahi Ganduje, Aminu Ado Bayero a Kano
Lokacin da Sarki Aminu Ado Bayero ke bude masallaci a Kano. Hoto: Aminu Dahiru
Source: Facebook

Hadimin Abdullahi Ganduje kan yada labarai, Aminu Dahiru Ahmad ya wallafa hotunan da aka dauka a wajen taron a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

An 'gano' dalilin zargin Amurka kan Kwankwaso bayan martani ga matakin Trump

Aminu Ado Bayero ya bude masallaci a Kano

Mai martaba Sarki Aminu Ado Bayero ya bude katafaren masallacin jumu'a da Gidauniyar Ganduje ta gina a unguwar Bachirawa a karamar hukumar Ungoggo a Kano.

Rahotanni sun nuna cewa masallacin da Aminu Ado Bayero ya kaddamar yana hade da makarantar Islamiyya da bangaren ibada na mata.

An bayyana cewa gidauniyar raya addinin Musulunci ta Ganduje ce ta dauki nauyin ginin masallacin karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Ganduje ya damka wa Sheikh Triumph masallacin

Ganduje ya sanar da cewa Sheikh Lawal Abubakar da ake kira Triumph ne zai kasance limamin masallacin da kuma rikon ragamar kula da makarantar Islamiyyar.

Sheikh Lawal Triumph fitaccen malamin addini ne a jihar Kano wanda a kwanakin baya aka yi zama da shi da kwamitin shura na jihar kan wasu zarge-zarge.

Sheikh Lawal Triump tare da Abdullahi Ganduje
Sheikh Lawal Triumph na gaisawa da Abdullahi Ganduje. Hoto: Aminu Dahiru
Source: Facebook

Ayyukan alherin gidauniyar Ganduje a Najeriya

A bayyana cewa gidauniyar raya addinin Musulunci ta Ganduje ta shafe sama da shekaru 30 tana hidima ga al'umma musamman abin da ya shafi addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Da mamaki: Bulama ya ga kuskuren amurka kan zargin kwankwaso da matsawa kiristoci

Hadimin Ganduje ya bayyana cewa aikin gidauniyar ya hada da gina makarantu, masallatai, shiryawa da daukar nauyin gasar karatun Al-Qur'ani mai girma, musuluntar da maguzawa da sauran su.

'Yan siyasa da malamai sun hallara

Taron ya samu halartar Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila da Alhaji Murtala Sule Garo da Hon. Alhassan Ado Doguwa.

Sanata Kabiru Gaya da Hon. Mukhtar Ishaq Yakasai da Umar Abdullahi Umar Ganduje da Muhammad Garba da sauran muhimman mutane sun halarci taron.

Malam Umar Shehu Zariya ya wallafa a Facebook cewa malaman Musulunci da-dama sun je wajen.

Sheikh Ibrahim Khalil, Sheikh Abubakar Kandahar, Sheikh Abba Adam Koki, Sheikh Nazifi Bichi da Sheikh Alibaba Fagge na cikin mahalarta bude masallacin.

Uba Sani ya yi kira ga malamai

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi kira ga malamai game da abubuwan da ya kamata su mayar da hankali a kai a Ramadan.

Gwamnan ya bayyana cewa akwai bukatar malamai su yi kira ga zaman lafiya lura da halin da Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Uba Sani ya yi magana ne ta bakin wakilinsa a wani taro da kungiyar JNI ta shirya game da watan Ramadan a jihar Kaduna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng