Atiku Ya Ki Shiru, Ya Dura kan Tinubu da EFCC a kan Kama El Rufa'i da 'Yan ADC

Atiku Ya Ki Shiru, Ya Dura kan Tinubu da EFCC a kan Kama El Rufa'i da 'Yan ADC

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi magana kan yunkurin cafke Malam Nasiru El-Rufa'i da aka yi a birnin tarayya Abuja
  • Atiku Abubakar ya yi zargin cewa hukumar EFCC da ke da alhakin yaki da cin hanci da rashawa ta fi mayar da hankali kan 'yan adawa
  • Ya yi gargadi da cewa hukumar EFCC za ta rasa kima a wajen jama'ar kasa idan ta cigaba da farautar masu adawa da gwamnatin Bola Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da yunkurin kama Malam Nasir El-Rufai a Abuja.

Da yake martani kan lamarin cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaransa ya fitar, Atiku ya nuna rashin jin daɗinsa kan yunƙurin da jami’an EFCC suka yi na kama El-Rufai ba tare da mutunta ƙa’idojin doka ba.

Kara karanta wannan

Atiku ya ziyarci El Rufai cikin dare bayan ya sha da kyar a filin jirgin sama

Atiku Abubakar tare da Nasir El-Rufa'i
Lokacin da Atiku Abubakar ya ziyarci Nasir El-Rufa'i a gidansa
Source: Facebook

Maganar Atiku kan kama El-Rufa'i

A wani sako da hadimin Atiku Abubakar, Paul Ibe ya wallafa a shafinsa na X, Mataimakin shugaban kasar ya yi tir da kokarin kama El-Rufa'i ba bisa ka'ida ba.

Ya ce:

“Duk da cewa ina goyon bayan yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar nan (kasancewar na taka muhimmiyar rawa wajen kafa hukumar EFCC),
"Ina nuna matuƙar damuwa da yadda ake mayar da kama mutane makamin siyasa da ke kai hari musamman ga shugabannin adawa, musamman ADC tun bayan kafuwarta,”

Ya ƙara da cewa yadda EFCC ke nuna ƙwazo fiye da kima wajen bibiyar jiga-jigan ADC ya kauce wa ainihin manufar da kundin tsarin mulki ya tanadar mata.

Nasir El-Rufa'i a gidansa da ke Abuja
Malam Nasir El-Rufa'i a gidansa bayan dawowa Najeriya daga Misra. Hoto: Bello El-Rufa'i
Source: Facebook

Atiku ya jaddada cewa ba a kafa EFCC domin ta zama makamin siyasa na shugaban ƙasa ko jam’iyya mai mulki ba, yana mai cewa:

“Idan aka ci gaba a kan wannan hanya, EFCC za ta rasa nagarta kuma ‘yancinta zai rushe.”

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya ce rikicin duniya da mai rai ake yi , zai buga da Tinubu da APC

Maganar Atiku kan tarihin EFCC

Atiku ya tuna da cewa kwamitin Uwais kan gyaran tsarin zaɓe ya ba da shawarar cewa ya kamata shugaban EFCC ya kasance karkashin Babban Alkalin Alƙalan Najeriya domin kare ‘yancin hukumar.

Sai dai tsohon mataimakin shugaban kasar ya nuna takaicinsa cewa kwamitin aiwatarwa da gwamnatin Umaru Musa Yar’Adua ta kafa bai ɗauki shawarar kwamitin Uwais kan ‘yancin EFCC ba.

Atiku ya tunatar da shugabannin EFCC da su rike matsayinsu da kyau maimakon son zuciya ko bin wata jam’iyya tare da mai da hankali kan muradun al’umma baki ɗaya.

El-Rufa'i ya ce yana nan daram

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa zai cigaba da adawa da APC.

Ya bayyana cewa har yanzu ba wanda ya fito ya ce ya saci kudin gwamnati a shekarun da ya shafe yana aiki a Abuja da Kaduna.

El-Rufa'i ya kara da cewa sun dauki aniyar kawar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da maye gurbinta da ADC a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng