Yunkurin Juyin Mulki: Kotu Ta Fusata game da Ci Gaba da Tsare Malamin Musulunci
- Gwamnatin Tarayya ta kasa gabatar da umarnin kotu da ke ba da damar tsare Sheikh Sani Abdulkadir Zaria
- Kotun Tarayya a Abuja ta umarci DIA ta kawo takardun, amma lauyan hukumar ya nemi karin lokaci kan haka
- Iyalan malamin sun danganta kama shi da kyautar Naira miliyan biyu da aka tura wa jagoran Fityanul Islam Tijanniyya da ake tsare da shi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta kasa gabatar da umarnin kotu da ke ba da izinin tsare fitaccen malamin addinin Musulunci.
Ana tsare da Sheikh Sani Abdulkadir Zaria, da ake zargi da hannu a shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
Wadanda aka shigar da kararsu kan tsare malami
Mai shari’a Peter Lifu na Kotun Tarayya da ke Abuja ya umarci Hukumar Leken Asirin Soji (DIA) da ta gabatar da umarnin kotu da aka ce an samu karkashin Dokar Gudanar da Shari’ar Manyan Laifuka (ACJA), cewar Daily Trust.
Umarnin ya biyo bayan alkawarin da lauyan hukumar, I. O. Odom, ya yi na cewa zai gabatar da takardun a gaban kotu.
A yayin sauraron karar kare hakkin dan Adam da lauyan shehin malamin, Sanusi Musa (SAN), ya shigar, an bukaci a saki wanda ake tsare da shi har zuwa lokacin yanke hukunci kan bukatar.
An shigar da karar ne a kan EFCC, DIA, Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, da kuma bankin Jaiz.

Source: Twitter
Alkali ya dage zaman kotu
Sai dai lokacin da aka kasa gabatar da umarnin kotun, mai shari’a ya dakatar da zaman daga karfe 11:00 na safe zuwa 3:00 na rana domin a samu damar kawo takardun.
Bayan komawa zaman, lauyan DIA ya roki kotu ta ba su karin lokaci, yana mai cewa ana tsare malamin ne a madadin Hedikwatar Tsaro.
Ya kara da cewa shugaban Kwamitin Bincike na Musamman (SIP) ya yi tafiya zuwa ketare, kamar yadda shugaban rundunar kula da da’a ya sanar da shi.
Lauyan EFCC ya goyi bayan wannan bukata, amma hakan bai gamsar da mai shari’a ba.

Kara karanta wannan
Tofa: EFCC ta gabatar da sababbin tuhume tuhume kan tsohon Akanta Janar, Ahmed Idris
Alkalin ya nuna mamaki kan yadda ba a iya fadin sunan kotun da ta bayar da umarnin ba, ko ranar da aka bayar da shi.
Daga karshe, kotun ta dage shari’ar zuwa ranar Juma’a domin yanke hukunci kan dambarwar da ake yi.
Majiyoyin iyali sun ce ana danganta matsalar malamin da Naira miliyan biyu da wani mabiyinsa ya tura wa asusun bankin jagoran kungiyar Fityanul Islam Tijanniyya da ake tsare da shi kan zargin juyin mulki.
An taso gwamnati a gaba kan tsare malami
Kun ji cewa cafke malamin addinin Musulunci da aka yi a jihar Kaduna ya fara tayar da hankula da neman bi masa hakkinsa kan ci gaba da tsare shi.
Masu kare haƙƙin ɗan Adam sun nuna damuwa kan ci gaba da tsare malamin a Zaria, Sheikh Sani Abdulkadir Khalifa kan zargin hannu a yunkurin juyin mulki.
An ce an kama malamin ne bisa zargin alaƙa da yunƙurin juyin mulki da ake dangantawa da wasu jami’an sojoji.
Asali: Legit.ng
