Amurka: 'Dan Majalisar Kano Ya Faɗi Mataki na gaba a kan Yi wa Kwankwaso 'Kazafi'

Amurka: 'Dan Majalisar Kano Ya Faɗi Mataki na gaba a kan Yi wa Kwankwaso 'Kazafi'

  • Dan majalisar tarayya mai wakilta Wudil da Garko AbdulHakeem Ado ya ce ba za su zuba ido a ci mutuncin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ba
  • Ya ce da zarar sun koma zaman majalisa, za su gatar da ƙuduri domin wanke jagoran Kwankwasiyya daga zargin da Amurka ke ƙoƙarin manna masa
  • Ya ce ba a nan za su tsaya ba, za su bukaci ‘yan majalisar Amurka su ba Najeriya haƙuri kan abin da ya kira ƙazafi da ɓata sunan nagartaccen mutum

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Hon. Abdulhakeem Kamilu Ado, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Wudi da Garko, ya bayyana cewa ba za su yi shiru kan zargin da a takwarorinsu a Amurka ke yi wa Rabi'u Musa Kwankwaso ba.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya fadi dalilin yi wa Kwankwaso bita da kulli a kasar Amurka

Ya ce zai gabatar da ƙuduri a gaban Majalisar Ƙasar na domin kare martabar Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso daga zargin da wasu ‘yan majalisar Amurka suka yi masa na muzguna wa Kiristoci.

Dan Majalisar Wudil da Garko ya ce za su tsaya wa Kwankwaso
Hon. AbdulHakeem Kamilu Ado, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: AbdulHakeem Kamilu Ado/NNPP
Source: Facebook

Wannan na kunshe a cikin wani sako da ya dauki nauyin wallafa wa a shafin Premier Radio, inda ya ce da zarar sun dawo daga hutu, za su fara aiki ka-in da na-in a kan batun.

'Dan majalisar Kwankwaso zai tsayawa Kwankwaso

Hon. Abdulhakeem Kamilu Ado ya bayyana cewa ba za su yi shiru a kan wannan magana ba, za su mika kurin da zai wanke Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso daga zargin da ake yi masa.

Ya ce:

"Da zarar Majalisar ƙasa ta dawo hutu, zamu gabatar da ƙuduri gamsashshe a gabanta domin wanke maigirma Jagora, tare da tilasta waɗancan ƴan Majalissa na Amurka su bawa Nigeria haƙuri a kan ƙazafin da suka yi ga ɗaya daga cikin mafi nagartar Mutanen ƙasar."

Hon. Abdulhakeem Kamilu Ado na ganin cewa zargin da aka yi wa jagoran ba daidai ba ne, kuma ya kamata a kare mutuncin sa a hukumance.

Kara karanta wannan

Bayan turo sojoji, Amurka za ta kafa 'tashar jiragen yaki' a a jihar Arewacin Najeriya

Ra'ayin jama'a a kan kudurin dan majalisa

Bayan kalaman ɗan majalisar, jama’a sun tofa albarkacin bakinsu a kafafen sada zumunta., inda wasu ke ganin hakan abu ne mai kyau.

Za a kai maganar Kwankwaso majalisar tarayya
Tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa kwankwaso
Source: Facebook

Mai kuɗi Abubakar ya ce:

“Misalin shugaba na gari ba mai mulki ba, shugaba mai tsoron Allah, mara cin hanci, mai hangen nesa, kuma mai kare talaka. ba wani ba ne face Engr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, Allah ya ƙara masa lafiya.”

Umar Kakangi ya ce:

"Ka ga halastaccen dan halak, ba munafukai irinsu Kawu Sumaila ba. Allah Ya dafa maka."

Basiru Shafiu ya bayyana cewa:

"Dan karaminsu kuma babbansu."

Sai dai Abubakar Aliyu Tsakuwar Dal ya ce:

"Wannan shashanci irin na Amurka ba abin damuwa ba ne saboda ba sa yabon mutanen kirki sai dai na banza."

Sakon mataimakin Gwamna kan Kwankwaso

A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi tir da kudirin da aka kai majalisar Amurka.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana daga India ana caccaka tsinke da Amurka

A cikin kudirin, yan kwamitin majalisar da suka hada da Riley Moore da wasy mutum hudu sun nemi a hukunta Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da kungiyoyin Fulnai makiyaya.

Mataimakin Gwamnan ya bayyana cewa akwai bukatar 'yan majalisar su tsame sunan Sanata Musa Kwankwasio daga cikin jerin wadanda za a sanya wa takunkumi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng