Ramadan: Gwamnan Sokoto Ya Tausaya wa Ma'aikata Ana daf da Fara Azumi
- Gwamna Ahmed Aliyu ya amince da fara biyan albashin Fabrairu daga 13 ga wata domin fara azumin Ramadan
- Gwamnan ya ce hakan zai ba ma’aikata damar shiga Ramadan cikin walwala ba tare da kunci ba
- Biyan albashin ya shafi ma’aikatan jiha, kananan hukumomi, da masu karɓar fansho a duk fadin Jihar Sokoto.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - A kokarin tallafawa ma’aikatan Jihar Sokoto, Gwamna ya amince da fara biyan albashin watan Fabrairun 2026 da muke ciki.
Gwamna Ahmed Aliyu ya ce ya yi haka ne domin ma'aikatan jihar su fara azumin watan Ramadan cikin kwanciyar hankali.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da shafin ofishin sakataren yada labaran gwamnatin jihar ya wallafa a Facebook a yammacin yau Alhamis 12 ga watan Fabrairu an 2026.
Yaushe ake da ran fara azumin Ramadan?
Al'ummar Najeriya na sa ran fara azumin watan Ramadan daga ranar 18 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da muke ciki.
Duk da cewa za a fara azumin a tsakiyar wata duba da tsadar rayuwa da ake ciki, ma'aikata a Sokoto ba za su sha wahala ba domin za su karbi albashinsu kafin fara Ramadan.
Musabbabin amince wa da biyan albashin ma'aikata
Sanarwar wacce daraktan yada labaran gwamnan, Abubakar Bawa ya sanya wa hannu ta ce an yi hakan domin taimakawa ma'aikata.
Ta ce Gwamna Ahmed Aliyu Sokoto, PhD, FCNA, ya ba da umarnin a fara biyan albashin ba tare da bata lokaci ba, daga ranar Juma’a, 13 ga Fabrairu, 2026.
Biyan albashin, kamar yadda aka saba, zai hada da ma’aikatan gwamnatin jiha, na kananan hukumomi, ma’aikatan Hukumar Ilimi ta Kananan Hukumomi da kuma tsofaffin ma’aikata masu karɓar fansho a dukkan fadin jihar.

Source: Original
Rokon da Gwamna ya yi ga ma'aikatan Sokoto
Gwamna Ahmed Aliyu ya yi kira ga ma’aikata da su mayar da martani ga wannan karamci ta hanyar kara himma, rikon gaskiya da jajircewa a aikinsu.
Ya ce:
“Ana sa ran ma’aikata su kasance masu zuwa aiki a kan lokaci, su yi aikinsu da ƙwazo da gaskiya, domin ta haka ne za mu cimma alkawuran da muka dauka wa al’ummar jihar.”
Gwamna Ahmed Aliyu ya jaddada kudurin gwamnatinsa na ci gaba da inganta harkokin mulki da tabbatar da dorewar cigaban Jihar Sokoto.
Haka kuma, ya mika godiyarsa ga al’ummar jihar bisa goyon baya da addu’o’in da suke bai wa gwamnatinsa a kowane lokaci.
Gwamna barranta kansa da yar TikTok, Rahama
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Jihar Sokoto ta yi magana bayan yada wani bidiyo da aka ba wata yar TikTok kyautar mota da shago.
Gwamnatin ta nesanta Gwamna Ahmed Aliyu daga kyautar mota da shago da aka ba matashiya Rahama Saidu wanda ake danganta wa da shi.
Mai magana da yawun gwamnan, Abubakar Bawa, ya ce kyautar aikin kai ne na wani mutum, Sanin Jaman, domin nuna goyon baya ga Ahmed Aliyu.
Asali: Legit.ng

