'Yan Bindiga Sun Sa Kayan Sojoji, Sun Sace Mata a Gidan Biki a Kano

'Yan Bindiga Sun Sa Kayan Sojoji, Sun Sace Mata a Gidan Biki a Kano

  • A ranar Laraba, 11 ga Janairun 2026 aka samu wani rahoto da ke cewa wasu 'yan bindiga sanye da kayan sojoji sun sace mata a wajen da ake biki
  • Bayanai da hukumomi suka fitar sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wani yankin kauyen Dabawa da ke karamar hukumar Shanono a jihar Kano
  • Sai dai dakarun Najeriya sun bi diddigin 'yan bindigar da suka sace mutanen kuma sun yi nasarar ceto wasu daga cikin wadanda aka sace a yankin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Wasu rahotanni sun nuna cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kutsa wani waje da ake shagalin biki sun sace mutane babu gaira babu dalili.

Dakarun runduna ta 3 ta sojin kasan Najeriya ta ceto mata takwas daga cikin mutane 10 da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka sace.

Kara karanta wannan

Hafsun sojoji ya fadi abin da ke jiran wadanda suka kitsa juyin mulki

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa an sace mutanen ne a wani wurin ɗaurin aure a ranar Laraba, a ƙauyen Dabawa da ke karamar hukumar Shanono a jihar Kano.

Yadda aka sace mutane a Kano

Wata majiya mai tushe a hedikwatar sojin kasa ta shaida cewa wasu ‘yan bindiga da ba a tantance adadinsu ba, waɗanda ake zargin sun sanya kayan soja, sun kai farmaki wurin bikin tare da yin awon gaba da wasu mahalarta.

Majiyar ta ce dakarun da aka girke a wani wurin kwanton ɓauna a kan hanyar Kogin Yankwada sun yi gaggawar matsawa zuwa yankin da lamarin ya faru bayan samun rahoton neman agaji.

Wani rahoto da Daily Post ta wallafa ya nuna cewa sojojin sun yi arangama da maharan da ke tserewa a ƙauyen Garu da ke kusa da jihar Katsina.

Dakarun sojojin Najeriya sun ceto mutane a Kogi
Yadda sojoji suka ceto wani mutum a Kogi. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

A cewar rahoton, sojojin sun bi sawun ‘yan bindigar har zuwa kan titin Katsina–Gidan Mutum Daya kafin su gudu su shiga wani daji.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi kisa yayin da suka sace limami, ladan da wasu mutane

Sojoji sun ceto mata a Kano

Sanarwar da aka fitar ta bayyana cewa dakarun Najeriya sun yi nasarar ceto wasu daga cikin wadanda aka sace kuma an mika su ga iyalansu.

“Yayin aikin, an samu nasarar ceto ‘yan mata takwas daga cikin waɗanda aka sace, kuma tuni aka haɗa su da iyalansu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano sauran da aka yi garkuwa da su.”

Inji sanarwar

Majiyar ta ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da ayyuka a yankin domin tabbatar da dawowar sauran waɗanda aka sace lafiya tare da hana sake faruwar hare-hare.

Sojoji sun ceto mutane a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun Najeriya na Operation Hadin Kai sun gwabza kazamin fada da mayakan kungiyar ISWAP a jihar Borno.

Sojojin sun kashe 'yan ta'addan ISWAP da dama yayin da wasu daga cikinsu suka gudu cikin daji bayan shan wuta a hannun jami'an tsaro.

Biyo bayan nasarar hallaka 'yan ta'addan, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa ta ceto wasu mutane da 'yan ta'addan suka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng