Gwamnan Gombe Ya Hada Kai da Tunisia, Ya Fadi Harkokin da Za Su Yi Tare
- Gwamna Inuwa Yahaya ya kulla yarjejeniyar zuba jari da kamfanonin kasar Tunisia domin inganta wasu muhimman fannoni a jihar Gombe
- Tawagar TUCAD za ta gudanar da ziyarar aiki zuwa Gombe domin tantance manyan ayyukan da za su samar da ayyukan yi ga matasa
- Gwamnan ya tabbatar wa masu zuba jarin cewa Jihar Gombe tana da yanayi mai kyau da dokoki wadanda za su kare dukiyoyinsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gombe - Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gana da wata tawagar masu zuba jari da bunkasa karkara karkashin kungiyar TUCAD domin bude sababbin hanyoyin zuba jari a fannoni masu muhimmanci ga jihar.
Ganawar, wadda aka gudanar a gidan gwamnatin Gombe dake Abuja tare da halartar jakadan Tunisia a Najeriya, Mohsen Antit, ta mayar da hankali ne kan ayyukan samar da ruwa, makamashi, sufuri, da kuma ababen more rayuwa na wasanni.

Source: Facebook
Hadakar Gombe da kamfanonin Tunusia
Wannan ganawa sharar fage ce kafin tawagar ta gudanar da ziyarar aiki zuwa Gombe domin tantancewa da kuma fara aiwatar da ayyukan da aka amince akai, in ji rahoton Tribune.
Mataimakin shugaban TUCAD, Issam Ben Youssef, ya bayyana cewa burinsu shi ne amfani da kwarewar kasar Tunisia a fannin ababen more rayuwa da masana'antu domin tallafa wa burin ci gaban jihar Gombe.
"Manufarmu ita ce mu kawo kwarewar Tunisia a fannin makamashi da tsarin samar da ruwa domin gina hadaka mai dorewa wadda za ta amfani kowane bangare," in ji Youssef.
Shugabannin kamfanoni daban-daban dake karkashin kungiyar sun yi bayani dalla-dalla kan kwarewarsu da kuma irin ayyukan da suka taba aiwatarwa a wasu kasashen.
An samar da wannan damar ne ta hanyar kamfanin African Network Centre, SARL Limited, a matsayin wani bangare na kokarin gwamnati na jawo masu zuba jari na kasashen waje.
Kudurin Gwamna Inuwa Yahaya
A nasa jawabin, Gwamna Inuwa Yahaya ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na samar da yanayi mai kyau, gaskiya, da kuma sauki ga masu zuba jari wadanda ke son gudanar da ayyuka na dogon lokaci a jihar.
A wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labarun gwamnan Gombe, Ismaila Uba Misilli ya fitar a shafinsa na Facebook, an rahoto gwamnan ya na cewa:
"Kofar jihar Gombe a bude take ga duk wani mai zuba jari, musamman a tsarin hadaka tsakanin kasashen Afirka.
Dabarun ci gabanmu ya dogara ne akan ababen more rayuwa, bunƙasa makamashi, samar da wadataccen ruwa, noma da ci gaban masana'antu. Muna sha'awar yin aiki tare da abokan hulɗa masu aminci waɗanda ke da hangen nesa iri guda da mu,"
Wannan hadaka za ta taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasan jihar da kuma fadada hanyoyin samun kudaden shiga ta hanyar masana'antu da bunkasa tattalin arziki.

Source: Facebook
Sanya hannu kan yarjejeniyar aiki
Babban abin da taron ya haifar shi ne sanya hannu kan takardun yarjejeniyar aiki (MoUs) tsakanin jihar Gombe da kungiyar masu zuba jarin ta kasar Tunisia.
Kwamishinan makamashi, Sanusi Ahmed Pindiga, da takwaransa na fannin ruwa da muhalli, Mohammed Saidu Fawu, ne suka sanya hannu a madadin hwamnatin jihar, yayin da Issam Ben Youssef ya sanya hannu a madadin kamfanoninsu.
Babban Lauyan jihar kuma kwamishinan shari'a, Zubair Muhammad Umar, ya shaida sanya hannun a madadin gwamnati, yayin da Alhaji Ahmed Shuaibu Gara-Gombe ya kasance shaida ga masu zuba jarin.
Gwamnatin Gombe ta samu karin N2.8bn
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce gwamnati ta yi nasarar rairaye wasu ma'aikata da aka tabbatar na bogi ne a jihar.
Gwamna Inuwa ya bayyana cewa wannan aiki da gwamnati ta yi ya bayar da daman samun rarar akalla N2.8bn da ake asara ta hanyar ma'aikatan.
Ya kara da cewa an yi wannan kora ne a fannin lafiya, kuma an gina da gyara cibiyoyin lafiya na farko 114 a ƙananan hukumomi da dama a Gombe.
Asali: Legit.ng


