Sanata Natasha Ta Tayar da Rigima, Ta Fadawa Shugaban Kwamiti Kalmomi Mara Dadi
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi cacar baki mai zafi da shugaban kwamitin kula da harkokin ma'adanai a zaman kare kasafin kudi
- Rahoto ya nuna cewa Natasha ta nuna fushin ta ne lokacin da shugaban kwamitin, Sanata Patrick Ndubueze ya nemi dakatar da ita
- Lamarin ya faru ne a zaman kare kasafin kudin ma'aikatar raya karafa ta Najeriya, wanda ya gudana ranar laraba a Abuja
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan (PDP, Kogi ta Tsakiya) ta yi musayar kalamai masu zafi da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Ma’adinai da Ƙarafa, Sanata Patrick Ndubueze.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 11 ga watan Fabrairun 2027 bayan kusan sa’o’i huɗu ana tattaunawa a zaman da kwamitin ya shirya domin kare kasafin kudi Ma’aikatar Raya Masana’antar Ƙarafa.

Source: Original
Daily Trust ta tattaro cewa zaman ya ɗauki zafi ne lokacin da Sanata Natasha ta ci gaba da gabatar da tambayoyinta, wanda hakan ya sa shugaban kwamitin ya dakatar da ita.
Kalamai masu zafi da Natasha ta fada
Wannan mataki ya jawo martani mai zafi daga sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, inda aka samu ɗan takaddama kafin daga bisani aka dawo da zaman cikin nutsuwa.
Sanata Natasha ta ce:
“Don Allah kada ka katse ni, har yanzu ina da abin da zan faɗa, kuma ina ganin ya kamata ka girmama ni.
"Wataƙila kana girmama ni, amma ina ganin ka riga ka nuna mini rashin girmamawa a yau. A’a, ba zai yuwu a mini haka ba. Ka yi magana sosai, ka bar ni in yi tawa. Ina da muhimmin abu da zan tattauna da minista.
“Ba laifi ba ne idan na yi magana sau ɗaya ko sau biyu. Wannan zaman tattaunawa ne kuma ka san cewa ba mu cika samun damar taro da minista ba,. Allah kaɗai ya san lokacin da za mu sake ganinsa a gaban kwamitin.”
Sanata ya maida martani ga Natasha
A martaninsa, shugaban kwamitin ya ce, "kin yi magana da yawa, kuma ke kinsan cewa na girmama ki.
Tun da farko, zaman kwamitin ya maida hankali kan yadda aka aiwatar da kasafin kuɗin 2024 da kuma shawarwarin 2025, kamat yadda Vangaurd ta kawo.
Sanata Natasha, wadda kamfanin Ajaokuta ke mazabarta, ta yi tambayar yadda aka tsara yarjejeniyoyin da kuma matakan da aka bi wajen tabbatar da gaskiya da tsari.

Source: Facebook
Yar majalisar ta ce:
“Na nemi a ba ni kwafin yarjejeniyar MoU domin in tabbatar an yi bincike daidai kafin amincewa amma aka hana ni, sai na dogara da bayanan da na samu daga wasu.”
An yi hayaniya a zama kare kasafin 2026
A wani labarin, kun ji cewa an yi cacar baki mai zafi a Majalisar Tarayya yayin kare kasafin kudin Ma’aikatar Noma ta 2026 kan rashin bayani da gaskiya.
Lamarin ya faru ne lokacin da Karamin Ministan Noma da Samar da Abinci, Sabi Abdullahi, ya gabatar da kasafin kudin ma’aikatar.
'Dan Majalisar Wakilai daga Jihar Rivers, Awaji-Inombek Abiante (APC), ya kalubalanci kasafin, yana cewa babu isasshen bayani, tsari da kuma adalci a cikin shirye-shiryen da aka gabatar.
Asali: Legit.ng

