To Fa: EFCC Ta Gabatar da Sababbin Tuhume Tuhume kan Tsohon Akanta Janar, Ahmed Idris

To Fa: EFCC Ta Gabatar da Sababbin Tuhume Tuhume kan Tsohon Akanta Janar, Ahmed Idris

  • Tsohon Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris ya fara fuskantar sababbin tuhume-tuhumen almundahana daga hukumar EFCC
  • Hukumar EFCC ta gurfanar da Ahmed Idris tare da wasu mutum hudu a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kan zargin karkatar da N109bn
  • Lauyoyin wadanda ake tuhuma sun nemi a dage zaman, kuma sun sanar da alkali cewa da yiwuwar a samu sulhu tsakanin bangarorin biyu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta sake bude shafin tsohon Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris.

Rahotanni sun nuna cewa Ahmed Idris, ya sake tsintar kansa cikin wata sabuwar tuhuma daga hukumar EFCC kan zargin sama da fadi da dukiyar kasa a lokacin da yake kan mukamin.

Ahmed Idris.
Tsohon Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris da hedkwatar EFCC da ke Abuja Hoto: EFCC Nigeria
Source: Facebook

EFCC ta sake taso Ahmed Idris

Kara karanta wannan

Hafsun sojoji ya fadi abin da ke jiran wadanda suka kitsa juyin mulki

Jaridar Aminiya ta kawo rahoton cewa hukumar EFCC na zarginsa da aikata laifuka shida da suka shafi almundahana tare da wasu mutum huɗu.

Idan baku manya ba, Ahmed Idris ya rike mukamin Akanta-Janar daga shekarar 2015 zuwa 2023, shekaru takwas na mulkin tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari.

Bayanai sun nuna cewa EFCC ta sake gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja tare da Mohammed Kudu Usman da kuma kamfanin Gezawa Commodity Market and Exchange Limited.

EFCC ta shigar da sababbin tuhume-tuhume

EFCC ta shigar da tuhume-tuhume shida da suka shafi almundanar kudade har Naira biliyan 109 kan tsohon Akanta-Janar da sauran wadanda ake zargi.

A zaman kotun, lauyan Ahmed Idris, Maliki Kuliya Umar, ya bayyana cewa wanda yake wakilta bai shirya ba domin bai samu wasu muhimman takardun da suka shafi shari’ar ba.

Ya jaddada cewa bisa doka, wajibi ne a bai wa waɗanda ake tuhuma isasshen lokaci da damar kare kansu yadda ya kamata. Saboda haka, ya roƙi kotun da ta ɗage shari’ar zuwa wani lokaci domin ba su damar shiryawa.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Sheikh Pakistan ya fadi dalilin murabus daga shugabancin NAHCON

Shi ma lauyan wanda ake ƙara na biyu da na uku, Farfesa Nasiru Aliyu SAN, ya mara wa wannan buƙata baya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

An fara neman sulhu da EFCC

Ya kuma bayyana cewa ya aika wasiƙu biyu zuwa ga shugaban EFCC domin duba yiwuwar warware batun ta hanyar sulhu ba tare da ci gaba da shari’a a kotu ba.

A nasa ɓangaren, lauyan EFCC bai nuna adawa da buƙatar lauyoyin ba, amma ya nemi kotu ta ba su damar samun takardun da suka ce ba su same su ba.

Shugaban EFCC.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Olanipekun Olukoyede Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Yusuf Halilu, ya bayyana cewa akwai yiwuwar a samu sulhu tsakanin ɓangarorin biyu. Daga ƙarshe, ya ɗage shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Maris, 2026.

EFCC ta tabo batun shari'ar Yahaya Bello

A wani rahoton, kun ji cewa hujumar EFCC ta bayyana cewa har yanzu ba a tabbatar tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello na da laifi ba har sai kotu mai cikakken iko ta tabbatar da hakan.

Hukumar ta jaddada cewa ana ci gaba da shari’ar da ake yi wa Yahaya Bello, kuma kotu ce kaɗai ke da ikon yanke hukunci kan ko yana da laifi ko a’a.

Ta kara da cewa gurfanar da mutum a gaban kotu kan aikata manyan laifuffuka na cin lokaci, domin ana bukatar gabatar da shaidu da hujjoji a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262