Daminar Bana: Kano da Jihohi 14 da Za Su Fara Samun Ruwan Sama da Wuri a Najeriya
- Hukumar NiMet ta yi hasashen samun ruwan sama da wuri a Kano, Neja da wasu jihohi 13 a kakar damina ta shekarar da muke ciki
- Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya gargadi manoman kasar da kada su yi gaggawar fara shuka don sun ga ruwa
- Ana sa ran samun fari mai tsanani har na tsawon kwanaki 21 a wasu jihohin Arewa wanda zai iya shafar ayyukan noma na bana
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar kula da yanayi ta kasa (NiMet) ta yi hasashen samun ruwan sama zai sauka da wuri a Kano, Neja, Rivers da wasu jihohi 12.
Ministan Sufurin Jiragen Sama da Harkokin Sararin Samaniya na Najeriya, Festus Keyamo, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Talata, 10 ga Fabrairu, 2026.

Source: Original
Minista ya gargadi manoman Najeriya
Ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoton hasashen yanayi na shekara-shekara (SCP) na 2026, kamar yadda rahoton Daily Trust ya nuna.
"Ina gargadin manoma da kada su yi gaggawar fara shuka iri yanzu, domin duk da ana samun yayyafi, damina ba ta kankama ba tukuna."
- Festus Keyamo.
Ministan ya jaddada cewa ana sa ran samun matsanancin yanayi tsakanin watan Maris zuwa Mayu, wanda zai iya shafar ayyukan yau da kullun a kasar.
Hasashen fara ruwan sama a Najeriya
Rahoton NiMet ya nuna cewa jihohin da za su samu ruwan sama da wuri sun hada da: Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom, Cross River, Benue, Kogi, Nasarawa, Oyo, da wasu sassan Kebbi, Niger, Jigawa, Katsina, Kano, Adamawa, and Taraba. Amma Borno za ta samu ruwa a latti.
Ministan ya bayyana cewa:
"Akwai yankunan da za su samu damina mai tsawo fiye da yadda aka saba, kamar su Legas, Kaduna, da kuma babban birnin tarayya Abuja."

Kara karanta wannan
NAHCON: Bayan murabus din Pakistan, an gano yadda Shettima ya sauya tunanin Saudiyya
Sabanin haka, ana sa ran samun gajeriyar damina a jihohin Yobe da wasu sassan Neja, wanda hakan ke bukatar manoma su dauki matakan kariya.
Haka kuma, za a samu karancin ruwan sama a jihohin Katsina da Zamfara idan aka kwatanta da yadda aka saba gani a shekarun baya da suka wuce, in ji rahoton Leadership.

Source: Twitter
Matsalar fari da daukewar ruwan Agusta
Hukumar ta yi gargadi kan samun fari mai tsanani na tsawon kwanaki 21 a jihohin Bauchi, Borno, Gombe, Jigawa, Katsina, Kano, Kebbi, Kwara, Nasarawa, Niger, Oyo, Plateau, Sokoto, Yobe, da Zamfara.
"Wannan fari zai dade sosai, don haka muna kira ga ma'aikatun gona da su ilmantar da manoma kan irin shukar da za su yi."
- Festus Keyamo.
Za a samu matsakaicin fari na kwanaki 15 tsakanin Maris zuwa Mayu a jihohin Oyo, Ogun, Ekiti, Kogi, Osun, Ondo, Edo, Ebonyi, Abia, Cross River, Delta, da wasu sassan Kogi da Kwara.
Har ila yau, za a samu dogon hutun ruwa a watan Agusta a jihohin Legas da Ogun, Ekiti da wasu sassan Oyo wanda zai iya daukar kwanaki 28.
Jihohin da za su samu ruwa mai yawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu damina mai tsawo fiye da yadda aka saba gani a jihohin Najeriya 13 a 2026.
Festus Keyamo, Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, ne ya bayyana hakan yayin gabatar da Hasashen Yanayi na Shekara-shekara (SCP).
Jihohi 13 da za su fu samun ruwan sama a 2026 sun hada da Legas, Benue, Enugu, Ebonyi, Ogun, Oyo, Nasarawa, Anambra, Kwara, Kebbi, Kaduna, Gombe da Taraba.
Asali: Legit.ng

