Jerin Manyan Malaman Musulunci 3 da Suka Tsaya ko Nuna Sha'awar Takarar Gwamna a Najeriya

Jerin Manyan Malaman Musulunci 3 da Suka Tsaya ko Nuna Sha'awar Takarar Gwamna a Najeriya

A 'yan makonnin da suka gabata ne alamu suka tabbatar da cewa tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami na shirin nemnan kujerar gwamnan Gombe a 2027.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Isa Ali Pantami, wanda ya yi aiki a gwamnatin marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nuna sha'awar neman takarar gwamnan jihar Gombe a inuwar jam'iyyar APC.

Pantami.
Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Pantamai a wurin sabunta rijistar APC Hoto: Abba Pantami
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa tsohon ministan ya sabunta katinsa na zama cikakken 'dan APC a mazabarsa da ke jihar Gombe a makon da ya gabata.

Sai dai wani abu da ya ja hankali tare da haddasa muhawara mai zafi game da yunkurin Pantami shi ne kasancewarsa babban malamin addinin musulunci a Najeriya.

Sheikh Pantami na daya daga cikin manyan malaman musulunci a Najeriya da ke bin tafarkin Sunnah, kuma duk da ya shiga siyasa, bai daina karantar da addini ba.

Kara karanta wannan

Shekaru 7 da ɗauke Dadiyata, El Rufai ya faɗi gaskiyar abin da ya sani

Mutane sun kasu biyu kan shiga siyasar Pantami, wasu na ganin malamin zai iya kawo sauyi babba a siyasar Najeriya, yayin da wasu ke ganin hakan zubar da kimar malunta ne.

Malaman Musulunci da suka yi sha'awar zama gwamna

Legit Hausa ta gano cewa ba Pantami ba ne malamin musulunci na farko da ya nuna sha'awa ko kuma ya yi takarar gwamna a Najeriya.

Bisa haka ne muka zakulo muku malaman musulunci da suka taba nuna sha'awa ko kuma suka tsaya takarar gwamna, ga su kamar haka:

1. Malam Ibrahim Khalil

Malam Ibrahim Khalil na daya daga cikin Malaman musulunci da suka taba yin takarar gwamna a Najeriya, ya nemi zama gwamnan jihar Kano a zaben 2023.

Sheikh Ibrahim Khalil, wanda shi ne shugaban majalisar malamai ta Kano, ya tsaya takarar gwamna ne karkashin inuwar jam'iyyar ADC a zaben 2023, amma bai samu nasara ba.

Fitaccen malamin yana daga cikin wadanda suka samu kuri'u da yawa a zaben da ya gabata idan aka cire manyan jam'iyyu, NNPP da APC.

Sheikh Ibrahim Khalil.
Shugaban Majalisar malamai ta jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil Hoto: Muhammad Cisse
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da BBC Hausa a baya-bayan nan, malamin ya ce zai ci gaba da neman takarar gwamna Kano har sai ya samu nasara.

Kara karanta wannan

El Rufai zai tsaya takarar shugaban Najeriya a 2027? Tsohon gwamna ya bada amsa

Ya kuma ce yana da tabbacin cewa jam'iyyar ADC, wadda ƴan adawa suka yi hadaka a cikinta da nufin kayar da APC a zaben 2027, za ta bayar da mamaki nan gaba.

2. Malam Abdulkadir Isa

Malam Abdulkadir Isa, daya daga cikin manyan malaman muslunci a jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas, ya nemi takarar gwamna a zaben 2023.

Malamin, wanda shi ne Babban Limamin Masallacin Gidan Talabijin na Jihar Adamawa (ATV), ya ce kaddara ce ta sa ya yanke shawarar tsayawa takarar gwamna domin share wa al'ummar jihar hawayensu.

Rahoton Aminiya ya tattaro cewa a lokacin da ya sanar da shirinsa kafin zaben 2023, Malam Abdulkadir ya ce dogaro da Allah da rungumar kowace kaddara ne suka sa ya yanke shawarar tsayawa takarar gwamna a Adamawa.

Limamin ya bayyana cewa ya fito neman takarar gwamnan ne da kyakkyawar niyya ta ceto jihar Adamawa daga halin da ta shiga.

Malam Abdulkadir Isa
Babban limamin masallacin gidan talabijin na jihar Adamawa, Malam Abdulkadir Isa Hoto: Aminiya
Source: UGC

3. Sheikh Isa Ali Pantami

Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Pantami ya nuna alamun fitowa takarar gwamnan jihar Gombe a babban zaben 2027.

Duk da bai yi wata sanarwa a hukumance ba kawo yanzu, amma tawagar matasa kuma mabiyansa, wacce ake kira da Pantamiyya ta fara yawon tallata malamin a kananan hukumomi Gombe.

Kara karanta wannan

"Sai mun tashi tsaye," Abin da El Rufai ya fadawa Atiku game da Tinubu a Abuja

A wani rahoto da Punch ta dauko, an ji Pantami na bayyana cewa ba wannan ne karo na farko da ya dhiga fagen siyasa ba, inda ya ce ya fara siyasa ne tun a 2001.

Sheikh Isa Pantami ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 4 ga watan Fabrairun 2026 yayin da yake jawabi a sakatariyar jam’iyyar APC ta jihar Gombe lokacin da ya je sabunta rijista.

Pantami.
Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami a masallacin Annooh da ke Abuja Hoto: Prof. Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Ya bayyana cewa shiga siyasa na da hanyoyi daban-daban, yana mai kwatanta hakan da harkar tsaro.

"Kamar yadda a fannin tsaro akwai hukumomi irin su DSS da NIA da ke aiki ba tare da kayan aiki ba, haka ma shiga siyasa na iya kasancewa ba tare da bayyanawa a fili ba.
"A wancan lokacin, muna daga cikin waɗanda ba sa sanya kayan aiki, amma mun jima a cikin siyasa tun 2001."

Abin da Pantami ya gamu da shi a ofishin APC

A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyar APC a Gombe ta yi karin haske kan zuwan Sheikh Isa Ali Pantami ofishin jam’iyyar domin sabunta katinsa a ranar 4 ga Fabrairun 2026.

Sakataren tsare-tsare na APC a Gombe, Ibrahim Musa Bakas ya tunawa Pantami cewa bai taba zuwa ofishin jam’iyyar ba a baya, har wasu ke dauka cewa dan jam’iyyar ADC ne kuma haka jama'a ke zata.

Ibrahim Bakas ya amince cewa Pantami ya taba yi wa jam’iyyar alheri a baya, yana mai cewa ya kawo gudunmawar da ba a taba samu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262