Wata Sabuwa: Majalisa Ta Yi Watsi da Kasafin Kuɗin Rundunar Sojojin Sama na 2026

Wata Sabuwa: Majalisa Ta Yi Watsi da Kasafin Kuɗin Rundunar Sojojin Sama na 2026

  • Kwamitin hadaka na majalisar dattawa da na majalisar wakilai ya yi watsi da kasafin kudin rundunar sojojin sama na shekarar 2026
  • Shugaban kwamitin, Sanata Osita Ngwu ya ce kudin da aka ware wa rundunar ya yi kadan kwarai wajen yaki da 'yan ta'adda a kasar
  • An kafa kwamitin mutum shida don tattaunawa da gwamnatin tarayya domin samar da kasafin kudin da zai wadaci ayyukan rundunar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kwamitin hada na kwamitocin Majalisar Dattawa da na Wakilai kan rundunar sojojin sama sun ƙi amincewa da kasafin kuɗin rundunar na shekarar 2026.

Shugaban kwamitin hadakar, Sanata Osita Ngwu, ya bayyana cewa ƴan majalisar sun haɗa baki wajen yin watsi da kasafin saboda ƙarancin kuɗi da kuma taɓarɓarewar tsaro a ƙasar.

Majalisar tarayya ta ki amincewa da kasafin kudin da aka warewa rundunar sojin sama a 2026
Shugaba Bola Tinubu ya na gabatar da jawabi a zauren majalisar dokokin kasar Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa majalisar ta ɗauki matakin ne yayin zaman kare kasafin kuɗi, inda aka duba yadda rundunar ta yi amfani da kudin shekarar 2025 da kuma buƙatunta na wannan shekara.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta zauna, ana son gwamnati ta cire tallafin wutar lantarki

Dalilan watsi da kasafin kuɗin NAF

Majalisar ta bayyana cewa kason da aka ware wa rundunar sojojin sama ya yi ƙasa da yadda za su iya gudanar da ayyukansu na yau da kullun a wannan lokaci.

Babban dalilin da ya sa aka ƙi amincewa da kasafin shine yadda rashin kuɗin zai shafi ƙarfin rundunar wajen yaƙi da ta'addanci.

Kwamitin hadar ya nuni da cewa rundunar sojin sama tana da muhimmiyar rawa wajen ba wa dakarun ƙasa kariya da kuma gudanar da bincike na sirri, don haka tana bukatar kasafin da yafi wannan.

Majalisa ta kafa kwamiti kan kasafin

Sanata Osita Ngwu ya jaddada cewa Nijeriya tana buƙatar mataki mai ƙarfi domin murƙushe ƴan ta'addada masu garkuwa da mutane.

Kwamitin ya lura cewa kusan kashi 70 cikin 100 na kasafin kudin da aka warewa ayyukan raya ƙasa na 2025 an mayar da su cikin na 2026 saboda yanayin tattalin arziki.

Sakamakon wannan matsala, kwamitin ya yanke shawarar kafa wani kwamiti na mutane shida domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Matar Aure, Khadija Jamilu ta dabawa mijinta wuka a mazakuta

Majalisar tarayya ta ce ayyukan sojojin sama suna bukatar kudi masu yawa domin yakar 'yan ta'adda.
Hafsan rundunar sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke yana sanya hannu kan jirgin M-346 a Italy. Hoto: @NigAirForce
Source: Twitter

Za a kara kasafin rundunar sojin sama

Wannan kwamitin zai gana da gwamnatin tarayya, ofishin kasafin kuɗi, da kuma shugabannin majalisar tarayya domin sama wa rundunar kasafin da zai biya bukatunta.

An ba sabon kwamitin aikin samar da sabon tsarin kasafi wanda za a sake gabatarwa kwamitin haɗaka domin dubawa da kuma amincewa da shi.

Majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ba da haɗin kai wajen ƙarfafa tsarin tsaron ƙasar domin kare rayukan ƴan Nijeriya cikin gaggawa.

Manyan bangarori a kasafin 2026

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 na N58.18trn gaban majalisar kasa a Disamba, 2025.

Kasafin kudin shekarar 2026 da shugaban kasa ya gabatar ya jaddada muhimman manyan bangarori huɗu: tsaro, ilimi, lafiya da ababen more rayuwa.

A cewar Shugaba Bola Tinubu, waɗannan fannoni suna da alaƙa da juna, kuma su ne ginshiƙin hanyar Najeriya zuwa haɓakar tattalin arziƙi mai dorewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com