Dan Bindiga da Ya Kashe Musulmi 57 a Masallaci Ya Fadi dalilin Amsa Laifinsa

Dan Bindiga da Ya Kashe Musulmi 57 a Masallaci Ya Fadi dalilin Amsa Laifinsa

  • Wani dan ra’ayin wariyar launin fata da ya kashe al'ummar Musulmai 51 a masallatai biyu a New Zealand ya fara korafi
  • Dan bindigan ya nemi a sake masa shari’a bayan shekaru bakwai da yanke hukunci game da barnar da ya yi
  • Brenton Tarrant ya ce lokacin da ya amsa laifinsa, yanayin kurkuku ya lalata masa lafiyar kwakwalwa, don haka bai yanke shawara cikin nutsuwa ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Wellington, New Zealand - Wani mai ra’ayin wariyar launin fata da ya kashe Musulmai 51 a masallatai biyu a kasar New Zealand ya ce bai da hankali lokacin da ya amsa laifi.

Rahotanni sun ce Brenton Tarrant, mai shekaru 35, ya bayyana hakan ne yayin da ya nemi kotu ta soke hukuncin da aka yanke masa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Bayan turo sojoji, an hango abin da Amurka za ta yi a zaben Najeriya na 2027

Wanda ya lashe Musulmi a masallaci ya bukaci sake masa shari'a
Dan bindiga da ya kashe Musulmi a New Zealand, Brenton Tarrant. Hoto: John Kirk-Anderson - Pool.
Source: Getty Images

Tarrant, dan kasar Australia, ya bayyana gaban kotu a Wellington ta hanyar bidiyo domin neman sake shari’a kan laifukan da ake tuhumarsa, cewar BBC.

Yadda Brenton Tarrant ya kashe Musulmi 51

A watan Maris na shekarar 2019, ya kai hari a masallatai biyu a Christchurch yayin sallar Juma’a, lamarin da ya fi muni a tarihin kasar.

Ya yi amfani da makamai irin na sojoji masu harbi da sauri, sannan ya wallafa harin kai tsaye a kafar sadarwa ta hanyar kyamara a kansa.

Da farko ya musanta dukkan tuhume-tuhumen, amma daga baya ya amsa laifuffuka 51 na kisan kai, 40 na yunkurin kisa, da laifin ta’addanci.

Zargin da Tarrant ke yi wa gidan yari

A gaban kotu, Tarrant ya ce tsauraran matakan kurkuku sun lalata masa lafiyar kwakwalwa, har ya kasa yanke shawara mai ma’ana.

Ya ce bai kasance cikin yanayin tunani mai kyau ba lokacin da ya amsa laifinsa, saboda wahalhalun da yake fuskanta a gidan yari.

Kara karanta wannan

Alkawarin da Abba Kabir ya yi ga wadanda suka yi hatsari a Kano bayan jajanta musu

Wanda ya kashe Musulmi a bukaci sake zama kan shari'ar da ake yi
Kotun da ake shari'ar Brenton Tarrant a New Zealand. Hoto: John Kirk-Anderson - Pool.
Source: Getty Images

Kotu ka iya sake hukunci kan Tarrant

Kotun daukaka kara za ta duba ko yanayin tsarewarsa ya hana shi iya fahimta da yanke shawara cikin hankali lokacin shari’a.

A halin yanzu, Tarrant na zaman gidan yari har abada ba tare da damar beli ba, hukunci na farko irinsa a tarihin New Zealand.

An tsara sauraron karar daukaka karar na tsawon kwanaki biyar, kuma ana sa ran kotu za ta yanke hukunci kafin karshen mako.

Iyalan wadanda aka kashe sun halarci kotu, inda wani uba ya ce Tarrant yana bata lokaci da kudin al’umma ne kawai, cewar rahoton ABS News.

Lamarin ya jawo wa iyalan shiga tashin hankali duba da yadda ya raba su da yan uwansu Musulmi yanzu kuma ana maganar sake duba shari'ar da aka yi shekaru da suka wuce.

Pakistan: Bam ya tarwatse da Musulmi

Kun ji cewa wani dan kunar-bakin-wake ya kashe masallata 31 tare da jikkata wasu 169 bayan ya tayar da bam a babban birnin Pakistan.

Kara karanta wannan

Harin Kwara: Kungiyar CAN ta tura muhimmin sako ga Musulmi da aka hallaka

Wannan harin ya faru ne a wani masallacin mabiya mazhabar Shi'a da ke yankin Tarlai a daidai lokacin da suke gabatar da Sallar Juma'a.

Shugaban kasa da Firayiministan Pakistan sun bayyana harin a matsayin babban laifi ga dan adam yayin da aka ayyana dokar ta-baci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.