Shugabar kasar New Zealand ta haihu
Firai ministar kasar New Zealand Jacinda Ardern ta samu ‘karuwar 'ya mace ta farko mai nauyin kilogram 3.31.
Tarihi ya nuna cewa ita ce shugabar kasa ta biyu da ta haihu akan mulki a zamanin nan.
Shugabar kasar wacce ke da shekaru 37 a duniya ta dauki hutun sati shida domin ba abunda ta haifa kulawa ta musamman sannan kuma ta mika ragamar mulki ga mataimakin shugabar kasar Winston Peters.
Sai dai ta ce za ta ci gaba da sa ido a kan yadda za a tafiyar da harkokin gwamnati.
Mai jegon ita ce firai minista mafi kankantar shekaru da aka samu a kasar tun bayan shekarar 1856.
KU KARANTA KUMA: 2019: Manyan jam’iyyun siyasa 2 sun hade don su kwace mulki daga APC
A shekarar 1990, Benazir Bhutto ta haifi 'ya mace tana rike da mukamin firai ministar Pakistan, kuma ita ce haihuwar farko da wata zababbiyar shugabar kasa za ta yi a lokacin.
Madam Ardern ta kuma haifi jaririyarta ne a ranar da aka haifi marigayiya Benazir Bhutto.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng