Majalisar dinkin duniya ta fara yakar masu kyamar Musulmi a duniya
Majalisar dinkin duniya ta yi jan kunne akan yadda matsalar kyamar Musulmi kara zafafa a duniya. Wannan jan kunne na zuwa ne a kasa da wata guda bayan kaiwa Muslulmi mumunan hari a kasar New Zealand wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum 50 a masallatai biyu.
Babban sakataren majalisar, Antonio Guterres ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya gabatar a jami’ar Al-Azhar da kekasar Masar, yayinda yake zantawa da Shugaban jami’ar, Sheik Ahmed al-Tayeb.
Guterres ya ce, duniya na fama da matsalar tsananin kyamar Musulmi da kyamar Yahudawa da nuna wariyar launin fata har ma da kyamar baki.

Asali: UGC
Sakataren ya tabo batun harin da wani mai rajin fifita farar fata ya kai a Masallatan New Zealand da kuma harin da aka kai wa Yahudawa a Majami’arsu da ke Pittsburgh, harin da aka bayyana a matsayin mafi muni kan Yahudawa a tarihin Amurka.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kungiyar ASUU reshen jiha ta sanar da shiga yajin aikin sai baba-ya-gani
Guterres da ke ziyarar kwanaki biyu a Masar, zai gana da shugaban kasar Abdel Fattah al-Sisi.
A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahaoto cewa Shugaban hukumar lafiya na jihar Niger, Usman Ndanusa, ya tabbatar da mutuwar mutane takwas, wanda cutar Sankarau ta kashe a karamar hukumar Borgu da ke jihar Niger.
Mista Ndanusa, wanda ya ke likita, shine ya bayyana hakan a lokacin da ya ke tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a yau Laraba 3 ga watan Afrilu, a garin Minna babban birnin jihar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng