Hankula Sun Tashi bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Jami'an Tsaro a Katsina, an Yi Kisa

Hankula Sun Tashi bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Jami'an Tsaro a Katsina, an Yi Kisa

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan jami'an tsaro na rundunar Community Watch Corps (C-Watch) a jihar Katsina
  • Tsagerun 'yan bindigan sun shirya kwanton bauna ne dai ga jami'an tsaron lokacin da suke kan hanyar tafiya zuwa wani kauye
  • An kashe jami'in tsaro tare da jikkata wani daban yayin artabun da aka yi a kan hanyar zuwa wani kauye da ke karamar hukumar Musawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Majiyoyi a jihar Katsina sun tabbatar da harin da 'yan bindiga suka kai kan jami'an tsaro na rundunar Community Watch Corps (CWatch).

'Yan bindigan sun hallaka jami'in tsaro na rundunar C-Watch tare da jikkata wani bayan sun kai harin musu kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Musawa ta jihar Katsina.

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro a Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Ana wata sai ga wata: 'Yan bindiga sun sake kai hari coci, sun sace masu ibada

'Yan bindiga sun kai hari ga jami'an tsaro

Rahotanni sun nuna cewa a ranar Lahadi, 8 ga Fabrairu, da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, an samu kiran gaggawa game da harin da aka kai wa ’yan C-Watch yayin da suke kan hanyar tafiya daga ƙauyen Dangani zuwa ƙauyen Dan Ali.

A yayin harin, wani jami’i mai suna Anas Yushau, mai shekaru 35, ya rasu sakamakon harbin da aka yi masa, yayin da wani jami’i, Nura Nasiru, mai shekaru 37, ya samu munanan raunukan harbin bindiga.

’Yan bindigan sun kuma tsere da bindiga guda ɗaya ta jami'an tsaron na rundunar C-Watch.

'Yan sandan Katsina sun kai dauki

Rundunar ’yan sanda ta gaggauta tura tawagar haɗin gwiwa ta tsaro, tare da haɗa kai da ofisoshin ’yan sanda na kananan hukumomi makwabta domin rufe hanyoyin tserewa.

An kai gawar mamacin zuwa babban asibitin gwamnati na Musawa, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa, yayin da wanda ya jikkata ke ci gaba da samun kulawar likitoci.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi kisa yayin da suka sace limami, ladan da wasu mutane

A halin yanzu, ayyukan tsaro na ci gaba domin bin sawu da cafke waɗanda suka kai harin.

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a Katsina
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga

'Yan bindiga sun sace limamin masallaci

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wasu mutanen da suka fita neman na abinci a jihar Plateau.

'Yan bindigan sun yi awon gaba da wani limamin masallaci, ladan dinsa da sauran wasu mutane da suka fita yin gawayi cikin daji a karamar hukumar Wase.

Mazauna yankin sun bayyana cewa an kai wa mutanen hari ne a bayan gari yayin da suke tsaka da samar da gawayi don sayarwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng