Rahoto: An Gano Ayyukan Gwamnatin Tinubu 92 da Aka 'Karkatar da Kudin' a Jihohi 5

Rahoto: An Gano Ayyukan Gwamnatin Tinubu 92 da Aka 'Karkatar da Kudin' a Jihohi 5

  • An fara bankado ayyukan damfara a aka fitar da kudadensu a karkashin gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
  • A wani rahoton bibiyar ayyukan raya kasa da aka fitar, an gano muhimman ayyuka 92 da aka sa rashin gaskiya wajen aiwatar da su a jihohi 5
  • Rahoton ya kuma tattaro ayyukan da gwamnatin tarayya ta samu nasarar kammalawa, wanda ya hada da shirye-shiryen tallafi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wani sabon rahoton tabbatar da gaskiya da bin diddigin ayyukan da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Tinubu, ya yi tone-tone.

Rahoton ya bankaɗo ayyukan da aka watsar, waɗanda ba a kammala ba, da kuma ayyukan zamba da yawa a karkashin gwamnatin Tinubu.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: a@aonanuga1956
Source: Facebook

Premium Times ta tattato cewa an saki rahoton bibiyar ayyukan na shekarar 2024/2025 wanda Tracka (shirin sanya idanu na BudgIT) ya fitar a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An samu gawarwakin mawakan yabon addini 4 a wani irin yanayi

An bankado ayyukan zamba a mulkin Tinubu

Binciken ya nuna cewa ayyuka 92 na gwamnatin tarayya, waɗanda darajarsu ta kai Naira biliyan 15.07, an aiwatar da su ne ta hanyar zamba.

Haka zalika, rahoton ya gano cewa akwai wasu ɗaruruwan ayyukan da har yanzu ba a kammala ba ko kuma ba a ma fara su ba duk da an sanya su a kasafin kuɗi.

Rahoton ya bayyana cewa ya sanya idanu kan ayyuka 2,760 a cikin jihohi 28, kuma ya gano yadda aka yi zamba a cikinsu wasu, wasu kuma aka yi fatali da su.

Abubuwan da bincike ya gano a jihohi 5

Sakamakon binciken ya nuna cewa ayyuka 1,438 ne kawai aka kammala, ana kan yin wasu 660 yayin da ba ma ba a fara ayyukan 471 ba kwata-kwata, sai kuma 99 da aka yi watsi da su bayan an fara.

Rahoton ya ayyana ayyuka 92 da na damfara saboda karkatar da kuɗaɗen, canza wurin ayyukan ba bisa ka'ida ba, cire kudin ayyukan da an riga an yi a kasafin shekarun baya, rashin kammala aiki, ko kuma yin aiki mara inganci.

Kara karanta wannan

Bayan haduwar mutanen Abba da na Ganduje, an gwabza rikici a taron APC a Kano

Tracka ta bayyana jihohin Imo, Legas, Kwara, Abia, da Ogun a matsayin jihohin da suka fi kowanne yawan irin waɗannan ayyuka n damfara, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.

Rahoton ya ce kashi 57.1% na dukkan ayyukan damfarar, waɗanda suka lakume Naira Biliyan 8.61 daga cikin jimillar Naira biliyan 15.07, suna cikin waɗannan jihohi biyar ne.

Ayyukan da gwamnatin tarayya ta kammala

Duk da ƙalubalen da aka fuskanta, rahoton ya nuna wasu ayyuka 15 da suka yi nasara sakamakon matsin lamba daga ’yan ƙasa.

Waɗannan ayyuka sun haɗa da inganta cibiyar kiwon lafiya ta Kaida Sabo, gyaran makarantar firamare ta Nawairudeen a jihar Filato, da kammala asibitin Ikirun.

Sauran sun hada da shirye-shiryen tallafa wa nakasassu a Katsina, da ayyukan kiyaye zaizayar ƙasa a Ribas da rijiyoyin burtsatse a Akwa Ibom.

Shugaba Tinubu.
Shugaba Bola Tinubu yana ganawa da ministoci a taron Majalisar zartarwa ta tarayya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Shugaban Tracka, Joshua Osiyemi, ya jaddada muhimmancin sanya idanu bin diddigin ayyuka gwamnati daga ɓangaren talakawa.

"Idan 5% na 'yan Najeriya za su sa ido kan ayyuka, za a iya kai ga sanya idanu kan kashi 50 na ayyukan ƙasa, wanda hakan zai rage cin hanci da rashawa tare da inganta rayuwar al'umma."

Kara karanta wannan

Ana batun dokar zabe, Ribadu ya aika da sakon gargadi ga 'yan siyasa

Gwamnatin Tinubu za ta fadada shirin CCT

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa shirin ta na bayar da tallafin kuɗi (CCT) ya amfani gidaje sama da miliyan 8.3 a fadin Najeriya.

Ministan jin ƙai da rage talauci, Dr Bernard Doro, ne ya bayyana hakan a babban taron ƙasa na farko kan harkokin jin ƙai da aka gudanar a Kuros Riba.

Dr Doro ya ce gwamnati tana da shirin faɗaɗa wannan tallafi domin ya isa ga gidaje miliyan 15 a faɗin ƙasar nan nan da wani ɗan lokaci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262