Masu Zanga Zanga Sun Mamaye Majalisar Dattawan Najeriya, Sun Bayyana Bukatarsu

Masu Zanga Zanga Sun Mamaye Majalisar Dattawan Najeriya, Sun Bayyana Bukatarsu

  • Masu zanga-zanga sun taru a kofar Majalisar Tarayya domin neman a sanya dokar dora sakamakon zaɓe kai tsaye ta yanar gizo
  • Majalisar Dattawa ta cire kudurin wajabta tura sakamako kai-tsaye daga sabon gyaran dokar zaɓe ta shekarar 2026 a makon da ya gabata
  • Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne domin kare hukumar INEC daga duk wata matsala ta yanar gizo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Zanga-zanga ta barke a babban birnin tarayya domin neman tabbatar da dora sakamakon zaɓe ta na'ura mai ƙwaƙwalwa daga hukumar INEC.

Masu zanga-zangar sun taru a ƙofar shiga majalisar dokokin kasar tarayya dake Abuja a yau Litinin, 9 ga Fabrairu, 2026.

Masu Zanga Zanga Sun Mamaye Majalisar Dattawan Najeriya, Sun Bayyana Bukatarsu
Peter Obi ya shiga zanga-zanga da wasu 'yan Najeriya ke yi a gaban majalisar dokokin kasar. Hoto: @IGBOnPROUD
Source: Twitter

Zanga-zanga ta barke a Abuja

Wannan zanga-zangar tana zuwa ne sakamakon matsayar da Majalisar Dattawa ta ɗauka kan batun dora sakamakon zaɓe ta hanyar nau'ra, in ji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Matar Aure, Khadija Jamilu ta dabawa mijinta wuka a mazakuta

An girke jami'an tsaro da dama da suka haɗa da ƴan sanda, sojoji, da jami'an NSCDC domin tabbatar da doka da oda yayin zanga zangar

Masu zanga-zangar sun nace cewa dole ne ƴan majalisa su fito fili su sanya kalmar "tura sakamako kai-tsaye" a cikin dokar.

Rigimar dokar zaɓe ta 2026

An samu gungumin korafe-korafe bayan da Majalisar Dattawa ta amince da gyaran dokar zaɓe ta shekarar 2022 a makon jiya.

Yayin zama na uku, majalisar ba ta amince da gyara sashe na 60, ƙaramin sashe na 3 ba, wanda zai tilasta dora sakamakon zai kai tsaye ta yanar gizo.

Wannan sashen zai buƙaci jami'an INEC su tura sakamakon kowace mazaɓa zuwa rumbun IREV kai-tsaye bayan an kammala ƙidaya da sanya hannu.

Maimakon hakan, majalisar tarayyar ta tsaya ne akan tsohuwar doka dake cewa jami'in zaɓe zai tura sakamako ta hanyar da hukumar INEC ta saba da ita.

Bayanin shugaban Majalisar Dattawa

Bayan surutai da suka biyo bayan dokar, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ba ƙin gyara dokar suka yi ba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kai sabon hari Benue, sun kashe fiye da mutum 10

Akpabio ya bayyana cewa majalisar ta bar dokar yadda take a 2022 ne kawai, inda aka cire kalmar "kai-tsaye".

Ya ce dalilin cire kalmar shi ne domin kauce wa matsalar yanar gizo, wadda ka iya zama harkar shari'a idan aka samu tsaiko.

A cewarsa, cire kalmar zai ba hukumar INEC damar yin amfani da dabarun da suka dace duba da ƙalubalen fasaha da kuma na tsaro.

Peter Obi ya jagoranci masu zanga zanga har gaban majalisar tarayya.
Peter Obi tare da Aisha Yesufu a yayin da suke zanga zanga a gaban majalisar tarayya. Hoto: @IGBOnPROUD
Source: Twitter

Peter Obi ya jagoranci 'yan zanga-zanga

Peter Obi, wanda ake sa ran zai kasance ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2027, ya jagoranci masu zanga-zangar har gaban ginin majalisar, rahoton Daily Trust ya bayyana hakan.

Ɗan siyasar wanda magoya bayansa masu tarin yawa suka take masa baya har da Aisha Yesufu, a halin yanzu suna kofar shiga majalisar.

“Mun wahala kan hatsarin. Ba mu son wani wata matsala. Muna son komai ya tafi daidai. Ku bari a yi zaɓen yadda ya kamata. Duk wanda yayi nasara, za mu amince," in ji Peter Obi.

Majalisa ta fitar da jadawalin zaben 2027

Kara karanta wannan

Dangote: Abin da zai ɗaga farashin litar man fetur zuwa N1000 a Najeriya

A wani labari na daban, mun ruwaito cewa INEC ta kammala tsara jadawalin babban zaben shekarar 2027 duk da cewa majalisar tarayya ba ta kammala gyaran dokar zabe ba.

Tuni dai hukumar ta miƙa dukkan buƙatunta ga majalisar domin tantancewa da kuma tabbatar da su kafin lokacin zaɓen ya gabato.

Duk da haka, INEC ta bayyana cewa za ta ci gaba da amfani da tsohuwar dokar zabe domin tabbatar da cewa shirye-shirye ba su tsaya ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com