Tashin Hankali: Matar Aure, Khadija Jamilu Ta Dabawa Mijinta Wuka a Mazakuta
- Wata matar aure, Khadija Jamilu ta soka wa mijinta wuka a mazakutarsa yayin wata takaddama da ta barke tsakaninsu
- Rundunar yan sandan jihar Yobe tana cigaba da neman matar da ta tsere yayin da aka garzaya da mijin nata zuwa asibiti
- Kwamishinan yan sanda ya yi tir da wannan lamari inda ya shawarci ma'aurata hanyoyin da za su bi don warware rikicin gida
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yobe - Wata matar aure mai shekara 18, Khadija Jamilu, ta soka wa mijinta wuƙa a mazakutarsa yayin da suke takaddama a gida.
Lamarin ya faru ne a garin Potiskum dake Jihar Yobe a sa'o'in farko na ranar Juma'a, 6 ga watan Fabrairu, 2026.

Source: Getty Images
Yobe: Amarya ta sokawa mijinta wuka
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu, in ji rahoton Punch.
Rundunar ta bayyana wannan lamari a matsayin wani babban laifi na cin zarafi da ya janyo wa mutum rauni mai tsanani.
Rundunar ƴan sandan ta karɓi kiran gaggawa ne da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin ranar Juma'a kan abin da ya faru da misalin ƙarfe 1:00.
An sanar da 'yan sandan cewa Khadija Jamilu ta yi amfani da wuƙa ne inda ta yi wa mijinta mai shekara 25 rauni mai zurfi a mazakutarsa.
Halin da ango ya shiga bayan harin
Bayan faruwar lamarin, Khadija ta tsere, inda har yanzu ƴan sanda suke ci gaba da neman inda take domin kamo ta.
Jami'an tsaro sun garzaya wurin da abin ya faru, inda suka kai mijin asibitin ƙwararru dake Potiskum domin neman taimakon gaggawa.
Daga baya an tura shi zuwa Babban Asibitin Tarayya (FMC) dake Azare, inda a halin yanzu yake karɓar magani sakamakon raunin.
Gargaɗi da shawarwarin 'yan Sanda
Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Emmanuel Ado, ya yi tir da wannan danyen aiki da matar ta aikata wa mijin nata, in ji rahoto Tribune.
CP Ado ya jaddada cewa ya kamata rayuwar aure ta kasance akan mutunta juna, haƙuri, fahimta, da kuma jure wa juna.
Ya nanata cewa kada a maida aure ya zama fage na cin zarafi, wulakanci, ko kuma amfani da tashin hankali wajen magance matsala.
Kwamishinan ya shawarci ma'aurata da su nemi shawarwarin ƙwararru tun kafin aure da kuma lokacin da aka shiga cikin zamantakewar.
Rundunar ta buƙaci ma'aurata su tuntubi iyaye, malamai, ko mutanen da suka amince wa idan matsala ta taso maimakon amfani da ƙarfi.

Source: Original
Kira ga shugabannin al'umma da iyaye
Rundunar ta yi kira ga shugabannin al'umma da iyaye da su wayar wa matasa kai kan yadda ake magance rigingimu a cikin ruwan sanyi.
Akwai buƙatar koyar da matasa dabarun sarrafa fushi da kuma muhimmancin gina dangantaka mai inganci tsakanin mace da miji a cikin gida.
Jami'an tsaro sun tabbatar wa jama'a cewa suna nan suna fafutukar ganin an kamo wadda ake zargi domin fuskantar shari'a akan abin da ta aikata.
Budurwa ta yankewa saurayinta mazakuta
A wani labari, mun ruwaito cewa, kotu ta yankewa wata budurwa hukuncin shekara sha uku a gidan yari, bayan an kama ta da laifin yankewa saurayinta mazakuta.
Budurwar mai suna Brenda Barattini, ta cirewa saurayin nata mai suna Sergio Fernandez mazakuta saboda ta gano yana nunawa abokanan shi bidiyon yadda suke kwanciya.
Shari'ar ta da aka yi a garin Cordoba, dake kasar Argentina, Barattini ta bayyana yadda ta yanke kusan kashi 90 cikin 100 na mazakutar saurayin nata Sergio.
Asali: Legit.ng


