Shikenan kuwa kowa ma ya huta: Budurwa ta yankewa saurayinta mazakuta bayan ta kama shi yana nunawa abokan shi irin kwanciyar da suke

Shikenan kuwa kowa ma ya huta: Budurwa ta yankewa saurayinta mazakuta bayan ta kama shi yana nunawa abokan shi irin kwanciyar da suke

- Wata budurwa ta yiwa wani tsohon saurayinta aika-aika, inda ta kusa hallaka shi

- Budurwar dai ta yankewa saurayin nata mazakuta ne gaba daya, bayan ta kama shi da wani laifi

- Budurwar ta bayyana cewa ta kama saurayin yana turawa abokanan shi bidiyo na yadda yake kwanciya da ita

An yankewa wata budurwa hukuncin shekara sha uku a gidan yari, bayan an kama ta da laifin yankewa saurayinta mazakuta, saboda ta gano cewa yana nunawa abokanan shi bidiyon yadda suke kwanciya.

Budurwar mai suna Brenda Barattini, mai shekaru 28, ta cirewa saurayin nata mai suna Sergio Fernandez mai shekaru 42 mazakuta shekaru biyu da suka gabata, inda ake tuhumar ta da laifin yunkurin kisa, hakan ya sanya aka yanke mata hukuncin shekaru sha uku a gidan yari.

Budurwar ta bayyana cewa ta shirya wannan aika-aikar a ranar 25 ga watan Nuwambar shekarar 2017, amma kuma bata da niyyar kashe tsohon saurayin nata.

KU KARANTA: Waiwaye: Hotuna da sunayen jaruman Kannywood da suka riga mu gidan gaskiya

Shari'ar ta da aka yi a garin Cordoba, dake kasar Argentina, Barattini ta bayyana yadda ta yanke kusan kashi 90 cikin 100 na mazakutar saurayin nata Sergio, a lokacin da ta rufe masa ido da tana yaudararsa da kissa ta mata.

Ta bayyanawa kotu cewa ta yi kokarin daukar fansa ne akan tsohon saurayin nata wanda ya dinga turawa abokanan shi hotuna da bidiyon ta a lokacin da suke kwanciya.

Ta bayyanawa kotun cewa abinda saurayin nata yayi mata ba daidai bane, domin ya bata mata suna ya kuma muzanta ta a idon duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel