Wata Sabuwa: Dan Majalisar Amurka Ya Yi Magana kan Batun Raba Najeriya

Wata Sabuwa: Dan Majalisar Amurka Ya Yi Magana kan Batun Raba Najeriya

  • Wani ɗan majalisar dokokin Amurka ya yi gargaɗin cewa yunƙurin ƙarfafa ra’ayin raba Najeriya zai iya ƙara tsananta matsalar tsaro a ƙasar
  • 'Dan majalisar ya ce hakan na iya jefa Kiristoci cikin haɗari musamman a Arewa ta Tsakiya, tare da bai wa ’yan ta’adda damar ƙara ƙarfi
  • Riley Moore ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya wajen yaƙar ta’addanci da rikice-rikice

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America — 'Dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya bayyana damuwa kan duk wani yunƙuri da ke neman rikitar da Najeriya ta hanyar ƙarfafa ra’ayin ’yan aware, yana mai cewa hakan zai cutar da al’ummar ƙasar baki ɗaya.

Moore ya bayyana hakan ne bayan kammala wata ziyara ta bincike da ya kai Najeriya, inda ya ce manufarsa ita ce fahimtar zarge-zargen cin zarafin Kiristoci da ake cewa na faruwa a wasu sassan ƙasar.

Kara karanta wannan

Komai a bayyane: Majalisar shari'a ta tono hadarin shugaban INEC ga Musulmi

Dan majalisar Amurka, Riley Moore
'Dan majalisar Amurka, Riley Moore yana jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ra’ayin ɗan majalisar kan batun tsaro

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X , Riley Moore ya ce rikitar da Najeriya na iya bai wa ƙungiyoyin ta’addanci damar faɗaɗa ayyukansu.

Punch ta wallafa cewa ya ce hakan zai sanya Kiristoci da sauran al’ummomi cikin babbar barazana ba a Najeriya kaɗai ba, har ma a nahiyar Afirka.

Moore ya bayyana cewa yayin ziyararsa, ya gana da jami’an gwamnati, shugabannin coci, ƙungiyoyin agaji da kuma ’yan gudun hijira a sassa daban-daban na ƙasar.

A cewarsa, tattaunawar ta ba shi damar fahimtar ƙalubalen da Kiristoci ke fuskanta musamman a Arewa ta Tsakiyar kasar.

Batun neman raba Najeriya

Moore ya ce a duk tattaunawar da ya yi, ba a taɓa kawo batun raba Najeriya ba. Ya jaddada cewa ƙarfafa ra’ayin ’yan aware ba zai taimaka wa Kiristoci ba, sai dai ya ƙara jefa su cikin haɗari a Arewa.

Kara karanta wannan

Yadda ƴan ta'adda suka rubuta wa Sarki wasiƙu kan shirin hari kafin hallaka Musulmai a Kwara

A cewarsa, Najeriya ƙasa ce mai muhimmanci a yankin Afrika, kuma duk wani yunƙuri na tayar da zaune tsaye zai iya shafar tsaron yankin gaba ɗaya.

Riley Moore da gwamnan jihar Filato
'Dan majalisar Amurka tare da Gwamnan jihar Filato. Hoto: @RepRileyMoore
Source: Twitter

'Dan majalisar ya ƙara da cewa rarrabuwar ƙasa na iya haifar da sabbin rikice-rikice da ’yan ta’adda za su yi amfani da su wajen cimma burinsu.

Haɗin gwiwar Amurka da Najeriya

Ɗan majalisar ya kuma yi tsokaci kan sabuwar yarjejeniyar haɗin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya. Ya ce yarjejeniyar wata muhimmiyar hanya ce ta magance matsalar tashin hankali da kuma ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.

Moore ya ce Amurka na da aniyar ci gaba da aiki tare da gwamnatin Najeriya domin rage matsalar tsaro da kare rayukan fararen hula ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.

Ganawa da Gwamnan jihar Filato

A wani labarin, mun rahoto cewa Rilley Moore ya gana da gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang inda suka tattauna batutuwan tsaro a Najeriya.

A cewarsa, tattaunawar ta mayar da hankali ne kan yadda za a zurfafa haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka musamman wajen magance matsalar tsaro.

Ya bayyana ganawar a matsayin mai fa’ida da hangen nesa, yana mai cewa zai ci gaba da aiki don tallafa wa duk ’yan Najeriya da ke fama da matsalar ta’addanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng