Nigeria @ 60: Ministan Buhari ya tabbatar da cewa ba zai yuwu a raba Najeriya ba

Nigeria @ 60: Ministan Buhari ya tabbatar da cewa ba zai yuwu a raba Najeriya ba

- Festus Keyamo ya ce duk mai so ya raba Najeriya aikin banza yake yi, saboda bazata taba rabuwa ba

- Karamin ministan kwadago da ayyuka ya ce duk tsanani da wahala mutuwa kadai ce zata rabamu

- Ministan ya ce Najeriya nada tarihin auratayya da harkokin arziki tsakanin kabilu, hakan zai sa a kasa rabuwa

Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da ayyuka ya ce "babu wanda zai iya raba Najeriya" saboda dalilai masu tarin yawa.

A ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba babban lawya kuma ministan Keyamo ya wallafa a shafin sa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, yana bayanin dalilan da zasu hana Najeriya rabuwa.

Keyamo yayi wannan maganar ne a ranar da Najeriya ta cika shekaru 60 da samun 'yanci daga Birtaniya.

KU KARANTA: Fyade: Kotu ta kori soja daga aiki, ta yanke masa hukuncin shekaru 5 a gidan yari

Festus Keyamo yace sakamakon auratayya da harkokin bunkasa arzikin da suka shiga tsakanin kabilu daban-daban, Najeriya bazata rabu ba.

Ministan, wanda dan jihar Delta ne, kuma bayerabe, ya ce har abada Najeriya na nan a matsayin kasa daya, mutuwa ce kadai zata raba ta.

Ya ce mutanen da ke neman raba kasarnan, su cigaba, amma bazasu taba samun nasara ba.

Nigeria @ 60: Ministan Buhari ya tabbatar da cewa ba zai yuwu a raba Najeriya ba
Nigeria @ 60: Ministan Buhari ya tabbatar da cewa ba zai yuwu a raba Najeriya ba. Hoto daga @FestusKeyamo
Source: Twitter

KU KARANTA: Da asusun bankunan fastoci muke amfani don guje wa jami'an tsaro - Dan damfarar yanar gizo

Kamar yadda ya wallafa, "a wannan lokacin, zan iya cewa kasar nan ba za ta taba rabuwa ba. Sakamakon tarihinmu, auratayya da ta shiga tsakaninmu da kuma harkokin bunkasa arziki, mutuwa ce kadai zata iya rabamu"

"Muna nan tare, har sai mun ciyar da Najeriya gaba. Barka da zagayowar shekarar samun 'yancin kai."

A wani labari na daban, Saleh Mamman, ministan wutar lantarki ya ce nan ba da dadewa ba, yan Najeriya zasu yi alfahari da yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gyara fannin wuta.

A ranar Laraba, ministan ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda yace, wannan mulkin ya samar da cigaba mai tarin yawa a ma'aikatar wutar lantarki. Mamman ya ce wannan mulkin a shirye yake da yayi gyara a bangarorin da ya lalace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel