An Fadi Wadanda Suka Taimaka aka Zubar da Jinin Musulmai kusan 200 a Kwara

An Fadi Wadanda Suka Taimaka aka Zubar da Jinin Musulmai kusan 200 a Kwara

  • Harin Woro da ya rikide zuwa mummunan kisa da ya bar daruruwan iyalai cikin alhini, yayin da ake ci gaba da gano gawarwaki bayan birne jama’a da aka yi
  • Bincike ya nuna ‘yan ta’adda sun san yankin sosai tare da samun bayanan sirri daga cikin al’umma, lamarin da ya sa suka kai farmaki kai tsaye ba tare da tangarda ba
  • Shugabannin gargajiya da na ƙaramar hukuma sun nuna damuwa kan rawar da wasu matasa da mazauna yankin ke takawa wajen ba da bayanai ga ‘yan ta’adda

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara – Al’ummar Woro da ke cikin ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara sun wayi gari cikin baƙin ciki da tashin hankali bayan wani mummunan hari da ‘yan ta’adda suka kai musu da dare.

Kara karanta wannan

Mamdani: An karanto tarihin Annabi SAW a tsakiyar Amurka, an nemi koyi da shi

Harin, wanda ya faru a daidai lokacin da al’umma ke cikin harkokinsu na yau da kullum, ya rikide zuwa kisan gillar da ya bar al'umma cikin jimami.

Yadda aka yi jana'izar mutane a Kwara
Wajen jana'iza a Kwara bayan kashe Musulmai da dama. Hoto: Reuters|BBC
Source: Facebook

Rahoton Vanguard ya nuna cewa zuwa yammacin Laraba, adadin wadanda suka mutu ya kai 162, yayin da wasu da dama suka bace, wasu kuma aka yi garkuwa da su.

Yadda aka kashe Musulmai a Kwara

Rahotanni sun tabbatar da cewa sama da ‘yan ta’adda 50 sun shiga Woro da misalin karfe 5:00 na yamma, inda suka rika kashe duk wanda suka gani tare da banka wa gidaje da shaguna wuta.

Wata mata daga cikin mazauna yankin ta ce:

“Sun rika shiga gidaje suna kashe mutane, wasu kuma sun kona su har ba a iya gane su ba. Har zuwa Alhamis da rana, ana ci gaba da gano gawarwaki.”

Tribune ta rahoto cewa ‘yan ta’addan sun sake dawowa da sassafe, inda suka yi kwanton-bauna suka kashe mutanen da ke kan hanyarsu ta zuwa sallar asuba.

Wadanda suka taimaka aka kai harin

Shugaban ƙaramar hukumar Kaiama, Alhaji Abubakar Abdullahi Danladi, ya bayyana harin a matsayin abin tausayi, yana mai zargin cewa akwai masu ba da bayanan sirri a cikin al’umma.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kausasa harshe kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya dauki mataki

Ya ce ‘yan ta’addan sun kai hari kai tsaye gidan shugaban kauyen, suka kashe ‘ya’yansa tare da amfani da motarsa wajen sace matarsa da wasu ‘yan uwa.

Taswirar jihar Kwara
Taswirar jihar Kwara a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Hakazalika, Sarkin Kaiama, Alhaji Omar Muazu, ya nuna damuwa kan yadda wasu matasa ke zama masu ba da bayanai ga ‘yan ta’adda, yana mai cewa hakan na kara ta’azzara matsalar tsaro a yankin.

Sarkin ya ce adadin wadanda aka birne zuwa yanzu ya kai 75, amma ana kyautata zaton adadin zai karu yayin da ake ci gaba da bincike a dazuka da sassan kauyen.

Yaron Shekau ya shirya harin kashe Musulmai

A wani labarin, kun ji cewa daya daga cikin yaran tsohon Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau mai suna Abubakar Saidu ne suka kai hari Kwara.

Abubakar Saidu da aka fi sani da Sadiku ya kasance tare da Shekau tsawon shekaru kafin a tura shi Arewa ta Tsakiya ta'addanci.

An bayyana cewa bayan zuwansa yankin, ya fara hada kai da manyan 'yan bindiga kamar su Dogo Gide kafin su samu sabani.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng