Limami Ya Kalli Bola Tinubu, Ya Yi Masa Wasu Addu'o'i a gaban Manyan Kasa a Abuja

Limami Ya Kalli Bola Tinubu, Ya Yi Masa Wasu Addu'o'i a gaban Manyan Kasa a Abuja

  • Babban limami a masallacin kasa, Farfesa Luqman Zakariyah ya yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu addu'o'i bayan sallar Juma'a a yau
  • Limamin ya yi wa shugaban kasa addu'ar samun nasara a mulkinsa yayin daura auren 'ya'yan karamin ministan tsaro, Bello Matawalle
  • Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya sanya albarka a cikin wadannan aurarraki da aka daura, ya ba ma’auratan zaman lafiya a rayuwarsu ta aure

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sha ruwan addu'o'i a wurin daura auren 'ya'yan karaminin ministan tsaro, Bello Matawalle.

Farfesa Luqman Zakariyah, limamin da ya jagoranci daurin auren ’ya’yan Bello Matawalle, a ranar Juma’a, ya bayyana Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin uba ga kowa.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin daura auren 'ya'yan Bello Matawalle Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X da yammacin yau Juma'a.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Tinubu ya sanya labule da Gwamna Uba Sani a Aso Rock Villa

Sanarwar ta ce babban limamin masallacin ya yi addu’a da fatan mulkin Shugaba Bola Tinubu ya zama sanadin dawo da fata ga marasa galihu a cikin al’umma.

Farfesa Zakariyah ya gudanar da wadannan addu’o’i ne yayin da Shugaba Tinubu ya halarci taron daurin auren ’ya’yan Matawalle da aka yi a Masallacin Kasa da ke Abuja.

Shugaban kasar São Tomé and Príncipe, Carlos Manuel Vila Nova, na daya daga cikin manyan baki da suka halarci daura auren.

Addu'o'in da limamin ya yi wa Tinubu

Da yake yi wa Shugaba Tinubu addu'a, limamin masallacin ya ce:

"Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya ba shugabanmu, wanda yake wakiltar kowa, kuma uba ga daukacin amare da ango, lafiya mai dorewa.
"Haka kuma muna rokon Allah ya ba shugabanmu tsawon rai, arziki, da nasara a lokacin mulkinsa. Muna addu’ar cewa zamaninsa ya kawo fata ga marasa galihu."

'Ya'yan Matawalle 9 da aka daura wa aure

Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, ya bada auren ’ya’yansa mata guda biyar, Maryam, Safiyya, Farida, Nana Firdausi, da Aisha.

Haka kuma, ’ya’yansa maza guda biyar,Ibrahim, Abdul Jalal, Surajo, Bello, da Fahad, su ma an daura masu aure a masallacin.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Tinubu, Abba, Ganduje suka halarci daurin auren ƴaƴan Matawalle 9

Shugaba Tinubu ne ya karbi amaren a madadin iyalan Matawalle zuwa cikin sabuwar rayuwarsu ta iyali

Masallacin kasa.
Shugaba Tinubu da wasu gwamnoni a masallacin kasa da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

An yi wa ma'aurata addu'ar zaman lafiya

Limamin ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya sanya albarka a cikin wadannan aurarraki da aka daura, ya ba ma’auratan zaman lafiya a rayuwarsu ta aure,, sannan ya albarkaci iyayensu da kakanninsu.

Taron ya samu halartar Gwamnonin jihohi, mambobin Majalisar Tarayya, mambobin Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), Hafsoshin Tsaro, wakilan kasashen waje, sarakuna, malaman addini, da dubban masoya.

Jiga-jigan da suka halarci daura auren Matawalle

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cikin wadanda suka halarci daurin auren yayan karamin ministan tsaro Bello Matawalle a babban masallacin kasa dake Abuja.

Daurin auren, wanda aka yi shi bayan sallar Jumu'ar yau, 6 ga Fabrairu, 2026, ya samu halartar manyan jami'an gwamnati da kuma jiga-jiganƴan siyasar ƙasar nan.

Bayan Tinubu, sauran manyan baƙi da suka halarta sun haɗa da Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, da ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya).

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262