Lauya Ya Roki Kotun Kano, Ta Saukaka wa Shehin Darika da aka Rufe a Kurkuku
- Babbar Kotun Jihar Kano ta sauƙaƙa sharuɗan beli da aka ɗaura wa Sheikh Ibrahim Makwarari da ake zargi da ƙirƙirar takardun mallakar filaye na bogi
- Tun da farko kotun majistare ta sanya belin Naira miliyan 20 tare da tsauraran sharuɗa, abin da ya sa wanda ake zargin bai samu damar cika belin ba
- Alƙalin Babbar Kotun ya rage belin zuwa Naira miliyan 5 tare da sauƙaƙa nau’in masu tsaya masa, bayan la’akari da roƙon da lauyoyinsa suka yi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Babbar Kotun Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Jamilu Shehu Suleiman, ta yanke hukuncin sauya sharuɗan beli da aka sanya wa malamin addini, Ibrahim Abdullahi Isa Makwarari.
Ana zargin malamin da ƙirƙirar takardun fili guda biyu da ke kan titin Ahmadu Bello Way a cikin birnin Kano, inda asalin takardun ke ɗauke da sunayen Kassim Usman Baba da Audu Yaro Fagge.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa hukunci ya biyo bayan ƙorafin da lauyoyin wanda ake zargin suka shigar gaban Babbar Kotun, suna cewa sharuɗan belin da kotun majistare ta gindaya sun yi tsauri fiye da kima.
Tuhumar da ake yi wa Ibrahim Makwarari
An gurfanar da Ibrahim Abdullahi Isa Makwarari ne a gaban Kotun Babban Majistare a ranar 21, Janairu, 2026, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Mustapha Sa’ad Datti.
Rahoton Daily Post ya bayyana cewa kotun majistare ta sanya belin Naira miliyan 20 tare da buƙatar mutane biyu masu tsaya masa.
Daga cikin sharuɗɗan, kotun ta ce dole ne ɗaya daga cikin masu tsaya masa ya kasance basarake tare da wasiƙar sahalewa daga Majalisar Masarautar Kano.
Kotun ta kuma buƙaci ɗayan mai tsaya masa ya kasance fitaccen ɗan kasuwa da ya mallakar fili ko gida da darajarsa ba ta gaza Naira miliyan 50 ba a cikin birnin Kano.
Roƙon lauyoyin Makwarari da matsayar kotu
Bayan shafe mako biyu ba tare da cika sharuɗɗan belin ba, lauyoyin wanda ake zargin, Barrista Abubakar Abdullahi Isa da Bashir Sabiu, sun garzaya Babbar Kotun Jihar Kano domin neman sauƙaƙa sharuɗan.
A yayin shari’ar, lauyoyin sun bayyana cewa laifin da ake tuhumar wanda suke karewa a kai laifi ne da doka ta amince da beli, kuma sharuɗan da kotun majistare ta gindaya sun yi tsauri matuƙa fiye da abin da doka ta tanada.

Source: Original
Sun roƙi kotun da ta yi adalci ta hanyar rage kuɗin beli da sauƙaƙa nau’in masu tsaya masa, domin bai wa wanda ake zargin damar amfana da ‘yancinsa na beli kafin ci gaba da shari’a.
An saukakawa Sheikh Makwarari beli
Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Mai shari’a Jamilu Shehu Suleiman ya yanke hukuncin rage kuɗin belin daga Naira miliyan 20 zuwa Naira miliyan biyar.
Kotun ta amince da lauyan wanda ake zargin, Barrista Abubakar Abdullahi Isa, ya zama ɗaya daga cikin masu tsaya masa, yayin da ɗayan zai kasance ɗaya daga cikin ‘yan uwansa.
Shehin Darika, Rigi Rigi ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa Shehin Darikar Tijjaniyya, Usman Kusfa Rigi Rigi ya rasu bayan fama da gajeruwar jinya da ya yi a jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa malamin ya kwanta dama ne a wani asibiti kuma an yi jana'izarsa a Zariya kamar yadda addini ya tanada.
Tun bayan sanar da rasuwar malamin, jama'a suka fara masa addu'o'i suna rokon Allah ya gafarta masa a kafafen sada zumunta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


