Jira Ya Kare: NECO Ta Fitar da Sakamakon Jarabawar Kammala Sakandare, SSCE 2025

Jira Ya Kare: NECO Ta Fitar da Sakamakon Jarabawar Kammala Sakandare, SSCE 2025

  • Hukumar NECO ta saki sakamakon jarrabawar SSCE External na 2025 inda dalibai 68,000 suka samu lashe darussa biyar ciki har da lissafi
  • NECO ta bayyana cewa an soke wasu cibiyoyin jarrabawa hudu sannan an dakatar da masu sanya ido biyar saboda magudin jarabawa
  • Rahoto ya yi bayanin yadda dalibai za su iya duba sakamakon su a yanar gizo ta hanyar amfani da katin duba sakamako na NECO

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Niger - Hukumar shirya jarrabawar ƙasa (NECO) ta saki sakamakon jarrabawar kammala sakandare ta masu zaman kansu (SSCE External) ta shekarar 2025 a yau Talata.

Shugaban hukumar, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ne ya sanar da sakin sakamakon da misalin ƙarfe 10:45 na safe a helkwatar hukumar dake Minna.

Hukumar NECO ta saki sakamakon jarabawar SSCE 2025
Dalibai suna zana jarawaba a wata makarantar sakandare a Najeriya. Hoto: Nony and Sons
Source: Facebook

Farfesa Wushishi ya bayyana cewa dalibai 96,979 ne suka yi rajistar jarrabawar, inda maza suka kai kaso 53.43 yayin da mata suka kai kaso 46.56, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Gwamnati ta bada umarnin rufe makarantu a fadin jihar Kogi

Sakamakon jarabawar NECO SSCE 2025

Daga cikin waɗanda suka yi rajista, mutum 95,160 ne suka samu damar zama domin rubuta jarrabawar a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Sakamakon ya nuna cewa wadanda suka zana jarabawar sun nuna ƙwazo sosai a fannonin lissafi da harshen Turanci a wannan shekarar.

A cikin mutum 93,425 da suka rubuta jarabawar Turanci, mutum 73,167 (kaso 78.32) sun samu makin nasara na credit zuwa sama.

Haka kuma, a cikin mutum 93,330 da suka zauna jarrabawar Lissafi, mutum 85,256 (kaso 91.35) sun samu credit zuwa sama.

Baki ɗaya, wadanda suka zana jarabawa 68,166 ne suka samu nasarar samun darussa biyar (5 credits) ciki har da Turanci da Lissafi.

Matsalar satar amsar jarrabawa ta karu

Farfesa Wushishi ya bayyana damuwa kan yadda aka samu ƙarin yawan maguɗin jarrabawa da kusan kashi 31.7 idan aka kwatanta da shekarar 2024.

Mutum 9,016 ne aka kama da laifuffuka daban-daban na satar amsa a lokacin gudanar da jarrabawar a sassan ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun bi sawun dan kasuwar Kano, sun ɗauke shi a jihar Nasarawa

Sakamakon hakan, hukumar ta sanya sunayen wasu masu sanya ido guda biyar a baƙar takarda saboda taimaka wa wajen maguɗi.

Waɗannan masu sanya idon sun fito ne daga Abuja, Kano, Adamawa, da kuma Jihar Ondo kamar yadda Farfesa Wushishi ya bayyana.

NECO ta ce ta rufe wasu cibiyoyi ta kuma dakatar da wasu masu tsaron jarabawa saboda sa hannu a magudi.
Dalibai suna zana jarabawar NECO yayin da wakilan ma'aikatar ilimi suke sanya ido. Hoto: @Neconigeria
Source: Twitter

Matakin da aka dauka kan cibiyoyin jarrabawa

Baya ga masu sanya ido, hukumar ta ba da shawarar soke rajistar wasu cibiyoyin zana jarrabawa guda huɗu baki ɗaya, in ji rahoton Leadership.

Waɗannan cibiyoyi sun haɗa da guda biyu a Jihar Neja, ɗaya a Jihar Yobe, da kuma ɗaya a Jihar Kano saboda sa hannu a maguɗin jarabawa.

Jarrabawar wadda aka gudanar tsakanin watan Nuwamba da Disamba 2025, tana ba ɗalibai damar inganta sakamakon su domin shiga jami'o'i.

Dalibai za su iya duba sakamakon su a yanar gizo ta hanyar amfani da katin duba sakamako na NECO a shafin hukumar.

NECO: Kano ta shiga gaban jihohi

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna farin cikinsa bisa yadda daliban Kano suka ci jarabawar kammala sakandire ta NECO a bana 2025.

Kara karanta wannan

Zargin lalata da matar aure: Magidanci ya sassara wani mutum da adda har lahira

A sakamakon jarabawar da hukumar NECO ta fitar yau Laraba, jihar Kano ta shiga gaban a jerin jihohin da suka samun sakamako mai kyau.

Gwamnatin Kano ta ce wannan nasara alama ce da ke nuna cewa matakan da Gwamna Abba ke dauka a fannin ilimi suna kan hanya, kwalliya tana biyan kudin sabulu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com