An Shiga Firgici a Gombe, 'Yan Bindiga Sun Farmaki Garuruwa 4, Sun Kashe Mutane
- 'Yan bindiga sun kashe wata mata mai juna biyu da dan uwanta sannan suka sace wasu mutane a wani mummunan hari da suka kai jihar Gombe
- Rahoto ya nuna cewa 'yan bindiga sun fara matsawa garuruwan Gombe da kai hare-hare da sace mutane, duk da kokarin da jami'an tsaro ke yi
- Shugabannin al'umma sun nemi gwamnati ta tura karin jami'an tsaro domin dakile ayyukan ta'addanci dake neman addabar yankunan Gombe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Gombe - Garin Pindiga dake ƙaramar hukumar Akko a Jihar Gombe ya shiga yanayin makoki sakamakon kisan ƴan uwa biyu da masu garkuwa suka yi.
Wannan mummunan lamari ya afku ne a ranar 28 ga watan Disamba, 2025, inda mahara suka farmaki gidan da 'yan uwan suke, da misalin ƙarfe 3:30 na dare.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun kai hari Gombe
Wadanda aka kashe sun haɗa da Yusuf Mohammed, mai shekaru 31, da ƙanwarsa Faiza Mohammed, mai shekaru 28, a gidansu dake kan titin Pindiga zuwa Kashere, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan
'Mutane sun tsere daga gidajensu': Halin da ake ciki a Gombe bayan harin ƴan bindiga
Rahotanni sun nuna cewa Faiza Mohammed tana da juna biyu na tsawon watanni bakwai lokacin da maharan suka harbe ta har lahira.
Maharan sun kuma yi awon gaba da ƙanwar su, Zainab Mohammed Yusuf, mai shekaru 16, bayan sun kashe yayyen nata biyu.
Daga nan maharan suka nufi gidan wani ɗan kasuwa, Alhaji Yayaji Abdullahi, inda suka sace matarsa da 'ya'yansa guda biyu.
Yawaitar hare-haren 'yan bindiga a Gombe
Wannan harin na Pindiga yana ɗaya daga cikin jerin hare-haren da ke ƙaruwa a yankunan Tumu, Pindiga, da Kashere da ke jihar Gombe a watan da ya gabata.
A ranar 13 ga Janairu, rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta sanar da dakile wani hari da ƴan bindiga suka so kaiwa ƙauyen Guda Lamido.
Duk da ƙoƙarin jami'an tsaro, a ranar 25 ga Janairu, mahara sun sake kai hari ƙauyen Rahama inda suka kashe Tela Ahmadu mai shekaru 70.
A ranar ne kuma suka farmaki ƙauyen Lambo suka sace mutane uku, amma jami'an tsaro sun yi nasarar ceto biyu daga ciki.

Source: Original
Martanin jami'an tsaro da na al'umma
Kakakin ƴan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa sun kashe ƴan bindiga uku a fafatawar da suka yi a ƙauyen Lambo, in ji rahoton The Sun.
Ya bayyana cewa:
“Jami'anmu sun yi nasarar ceto Babayo Garba da Malam Abba Musa, yayin da aka kashe ƴan bindiga uku a daji.”
Sai dai abin takaici, ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, Baayo Bayi, ya rasa ransa sakamakon harsashin da ya same shi yayin musayar wuta.
Shugabannin al'umma sun yi kiran gaggawa ga gwamnati da ta tura ƙarin jami'an tsaro domin kare gonakinsu da kasuwannin su daga lalacewa.
Sun yi gargaɗin cewa idan ba a dakile waɗannan ƴan bindiga ba, tattalin arziƙin yankin zai durƙushe sakamakon tsoron zuwa gona ko kasuwa.
Mutane 6000 sun tsere daga gidajensu
A wani labari, mun ruwaito cewa fiye da mutane 6,000 ne suka tsere daga gidajensu a garuruwan da ke karkashin masarautar Pingiga, jihar Gombe.
Rahoton ya nuna cewa al'ummar wadannan garuruwa sun yi hijirar dole ne sakamakon tsanantar hare-haren 'yan bindiga a cikin 'yan kwanakin baya.
Gwamnatin Gombe ta fara tantance wadanda hare-haren suka shafa a masarautar Pindiga domin samar musu da abinci da matsugunan wucin gadi.
Asali: Legit.ng
