Gwamna Abba da Ya Koma APC Ya Yi Sababbin Naɗe Naɗe, Ya Ɗaga Darajar Jarumar Fim

Gwamna Abba da Ya Koma APC Ya Yi Sababbin Naɗe Naɗe, Ya Ɗaga Darajar Jarumar Fim

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Abubakar Matawalle a matsayin sabon shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano
  • Fitacciyar jarumar Kannywood Aina’u Ade ta samu karin girma zuwa babbar mataimakiyar gwamna kan harkokin fina-finai
  • Gwamnan ya bukaci dukkan sababbin jami’an da su yi aiki tukuru domin ciyar da jihar Kano gaba da cimma muradun gwamnatinsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da sababbin nade-nade da karin girma a wasu muhimman hukumomin gwamnatin jihar.

Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Gwamna Abba Yusuf ya yi sababbin nade-naden mukamai a gwamnatin Kano
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a taron ba matasa tallafi. Hoto: @Kyusufabba
Source: Twitter

Gwamna Abba ya yi nade nade

Sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ta bayyana cewa Gwamna Abba ya nada Abubakar Matawalle a matsayin shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Matsayar majalisar dokokin Kano kan tsige mataimakin Gwamna Abba

Haka kuma, gwamnan ya amince da karin girman Yusuf Mukhtar zuwa matsayin babban sakatare a cikin ma’aikatan jihar Kano.

A fannin nishadi, fitacciyar jarumar Kannywood, Aina’u Ade, ta samu karin girma a karkashin wannan sabon tsarin na gwamnati.

An daukaka darajarta daga matsayin mai tallafawa gwamna zuwa matsayin babbar mai taimaka wa gwamna (SSA) kan harkokin masana'antar Kannywood.

Rahama Alhaji kuma an nada ta a matsayin shugabar cibiyar ba da horo kan yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.

Sanarwar ta kara da cewa an nada Abdulkadir Kankarofi a matsayin mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin jinkai.

Dukkan wadannan nade-nade da karin girma sun fara aiki ne nan take kamar yadda sanarwar ofishin gwamnan ta bayyana.

Kwarewar wadanda Abba ya nada

Dawakin Tofa ya bayyana Matawalle a matsayin gogaggen ma’aikaci wanda ya dade yana kula da harkokin aikin Hajji a jihar.

Matawalle ya taba rike mukamin babban sakatare na hukumar alhazai kafin ya yi ritaya daga aikin gwamnati a shekarar 2014.

Kara karanta wannan

Wasu kwamishinoni sun rikita gwamnatin Kano bayan komawar Abba APC? Gaskiya ta fito

Sanarwar ta ce:

"Matawalle kwararren ma'aikaci ne wanda ya nuna kwarewa wajen gudanar da ayyukan hajji tsawon shekaru da dama."

Game da Rahama Alhaji, mai magana da yawun gwamnan ya bayyana ta a matsayin kwararriyar lauya mai dimbin sani kan harkar shari'a da gudanarwa.

Gwamna Abba Yusuf ya daga darajar Aina'u Ade zuwa babbar mai taimaka masa
Aina'u Ade, fitacciyar jarumar Kannywood da Gwamna Abba ya kara wa matsayi a gwamnatin Kano.
Source: UGC

Karin girman jaruma Aina'u Ade

Shi kuwa karin girman da aka ba wa jaruma Aina’u Ade, ya biyo bayan kokarin da ta nuna ne a baya. Dawakin Tofa ya ce jarumar ta nuna kwazo sosai a matsayinta na mataimakiyar gwamna ta musamman a bangaren fina-finan Hausa.

Gwamna Yusuf ya bukaci dukkan wadanda aka nada da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu domin amfanin talakawan jihar.

Ya nanata cewa dole ne su nuna gaskiya da biyayya ga manufofin gwamnatinsa na "Kano First Agenda" a kowane lokaci.

Gwamnan ya jaddada cewa wannan garambawul an yi shi ne domin kara inganta ayyukan gwamnati da samar da sauki ga al'umma.

Kara karanta wannan

Bayan shiga APC, Abba zai kawo karshen rikicin Sanusi II da Aminu Ado Bayero

An yi sababbin nade-nade a Kano

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da sababbin nade-nade da karin girma ga wasu manyan jami’ai a jihar.

Darakta janar a kan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature D-Tofa ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 28 ga watan Janairu, 2026.

Daga cikin wadanda aka nada akwai Hon. Abdulkadir Balarabe Kankarofi (Alhajiji), wanda aka nada a matsayin mai ba gwamna shawara ta musamman kan harkokin jin kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com