Dandalin Kannywood: Jaruma Aina'u Ade ta zama amarya

Dandalin Kannywood: Jaruma Aina'u Ade ta zama amarya

Alamu masu karfin gaske na nuni da cewa tauraruwar nan ta fina-finan Hausa, Hajiya Aina'u Ade, wadda aka fi sani da Laila ta zama amarya a yan kwanakin nan da suka wuce.

Wannan kuma kamar yadda majiyoyin mu suka tabbatar mana cewa alamu masu karfi na nuni da hakan duk kuwa da ba'aga hotunan shagalin bikin nata a shafukan ta na dandalin sada zumunta ba.

Dandalin Kannywood: Jaruma Aina'u Ade ta zama amarya
Dandalin Kannywood: Jaruma Aina'u Ade ta zama amarya

KU KARANTA: Adam Zango ya nuna soyayyar sa ga Zainab Indomie

Legit.ng dai ta kula da cewa wasu dayawa daga cikin abokan sana'ar ta da kuma 'yan uwa da abokan arziki suna ta taya ta murnar yin auren a ciki da wajen dandalin sada zumuntar.

A bayan dai mun taba kawo maku labarin cewa jarumar yayin da ta ke zantawa da wakiliyar majiyar mu, ta bayyana cewa shi aure abu ne na Allah, duk lokacin da Allah ya kawo shi ko ka yi niyya ko ba ka yi niyya ba za ka yi shi ne.

To mu ma dai muna taya ta murnar yin auren tare kuma da fatan Allah ya bada zaman lafiya ya kuma bada zuri'a dayyiba ta gari.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel