An Yi Jina Jina tsakanin Sojoji da 'Yan Bindiga 100, an Kashe Kachalla Gwaska

An Yi Jina Jina tsakanin Sojoji da 'Yan Bindiga 100, an Kashe Kachalla Gwaska

  • Rahoto ya nuna cewa sojojin Najeriya sun yi artabu mai tsanani da ’yan bindiga a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara yayin wani samame na musamman
  • Rundunar ta ce ta lalata sansanin shahararren shugaban ’yan bindiga Gwaska Dan Karami, inda aka kashe ’yan bindiga da dama bayan samun sahihan bayanan sirri
  • Dakarun sojin kasa da na sama sun hada kai wajen kai harin, yayin da rundunar ta jaddada kudirinta na ci gaba da tarwatsa hanyoyin samar wa ’yan bindiga makamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara – Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da wani artabu mai tsanani da ’yan bindiga a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, yayin da sojojin ke aiwatar da wani samame karkashin Operation Fansan Yamma.

Kara karanta wannan

Ba rufa rufa: Sunayen mutum 40 da aka kama bisa shirin yi wa Tinubu juyin mulki

Bayanan da rundunar ta fitar sun nuna cewa an kai harin ne kan sansanin shahararren shugaban ’yan bindiga Gwaska Dan Karami, bayan samun sahihan bayanan sirri da ke nuna taruwar ’yan bindiga sama da 100.

Sojoji Najeriya a wani daji a jihar Zamfara
Sojoji yayin fafatawa da 'yan bindiga a dajin Zamfara. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

A sakon da ta wallafa a Facebook, rundunar ta ce duk da asarar rayukan wasu daga cikin sojoji, an samu gagarumar nasara ta fuskar tarwatsa sansanin ’yan bindiga da rage karfinsu a yankin.

Sojoji sun farmaki 'yan bindiga 100

Mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin kasa, bangaren Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya ce an dauki tsawon kwanaki ana sa ido kan sansanin kafin kai harin.

Osoba ya ce bayanan sirri sun nuna cewa ’yan bindiga sun taru ne domin shirya hare-hare kan al’ummomin yankin da kuma kan hanyoyin kai kayayyakin soji.

A cewarsa, a ranar 31, Janairu, 2026, dakarun sojin kasa tare da goyon bayan rundunar sojin sama ta Najeriya suka yi wa sansanin kwanton bauna, lamarin da ya haifar da artabu mai tsanani.

Dakarun Sojoji sun yi artabu da 'yan bindiga

Rundunar ta bayyana cewa ’yan bindiga sun yi yunkurin kewaye sojojin ta wasu hanyoyi, amma hakan bai yi nasara ba sakamakon karfin wuta da dabarun sojoji.

Kara karanta wannan

Barawon motar Naira miliyan 75 ya yi wa 'yan sanda barkwanci a Kano

Osoba ya ce an kashe ’yan bindiga da dama yayin artabun, yayin da wasu suka tsere dauke da raunukan harbin bindiga. Bayan kammala artabun, sojojin sun kona sansanin gaba daya.

Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa wasu daga cikin jaruman sojoji sun sadaukar da rayukansu a wannan artabu, sannan wata motar yaki ta kone bayan harbin roka daga bangaren ’yan bindiga.

Sojojin Najeriya a dazjin Zamfara
Dakarun Najeriya a bakin aiki a dajin Zamfara. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Matakan da sojoji ke kara dauka

Rundunar ta ce rundunar sojin sama na ci gaba da gudanar da hare-haren domin cafke ’yan bindigan da suka gudu, yayin da sojojin kasa ke ci gaba da rike iko da yankin.

Punch ta wallafa cewa Osoba ya jaddada cewa rundunar soji na girmama sadaukarwar sojojin da suka rasa rayukansu, tare da tabbatar wa al’umma cewa ba za ta ja da baya ba wajen yaki da ’yan bindiga.

Sojoji sun kai hare-hare Kwara

A wani labarin, kun ji cewa dakarun Najeriya sun kaddamar da sabon shirin kai hare-hare kan 'yan bindiga a Kwara da ake kira Operation Igbo Danu.

Rahotanni sun nuna cewa an kawo sabon shirin ne da nufin kakkabe 'yan bindiga da ke fakewa a dazukan jihar suna garkuwa da mutane.

A wani farmaki da sojoji suka kai cikin wasu dazukan jihar Kwara, sun yi nasarar fatattakar 'yan ta'adda tare da kashe wasu da dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng