Juyin Mulki: Yadda aka Tsara Harbe Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa

Juyin Mulki: Yadda aka Tsara Harbe Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa

  • Ministan tsaro, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa yana cikin mutanen da masu yunkurin juyin mulki suka sanya a jerin waɗanda za a harbe
  • Janar Musa mai ritaya ya ce wasu manyan jami’an gwamnati da fitattun mutane ma na daga cikin waɗanda aka tsara kashewa a yunkurin juyin mulkin
  • Yayi bayani ne bayan sojoji sun tabbatar da cewa jami’an da ake zargi za su fuskanci shari’a a gaban kotun soja bisa tanadin dokokin aikinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa shi ma yana cikin manyan mutanen da aka tsara kai wa hari a yunkurin juyin mulkin da ake zargin wasu jami’an soji sun yi.

Wannan bayani na zuwa ne kwanaki bayan rundunar soji ta tabbatar da cewa wasu daga cikin jami’an soji 16 da aka kama tun watan Oktoban 2025 za su fuskanci shari’a bisa zargin yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Ministan tsaro ya faɗi hukuncin da ke jiran sojojin, ya yi albishir ga iyalansu

Janar Christopher Musa mai ritaya
Ministan tsaro, Christopher Musa na yi wa jama'a bayani a taro. Hoto: General CG Musa
Source: Twitter

Janar Musa, wanda shi ne tsohon Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a shirin Sunday Politics na tashar Channels Television.

Yadda aka tsara harbe Ministan tsaro

A hirar, Ministan tsaron ya ce masu shirin juyin mulkin sun yi niyyar kama shi, kuma idan ya ƙi amincewa da hakan, za a harbe shi.

Punch ta rahoto ya ce:

“An shirya kama ni, kuma idan na ƙi, an shirya a harbe ni,”

Ya ƙara da cewa ba shi kaɗai ba ne aka sanya a jerin hare-haren, domin wasu manyan jami’an gwamnati da shugabanni ma an tsara kai musu farmaki.

Magana kan masu yunkurin juyin mulki

Janar Musa ya bayyana mutanen da ake zargi da shirya juyin mulkin a matsayin marasa hankali, yana mai cewa bai fahimci yadda suka yi tunanin za su iya tinkarar rundunar sojin Najeriya ba.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Abin da aka tanadar wa iyalan sojojin da suka yi yunkurin yi wa Shugaba Tinubu juyin mulki

“A ganina, waɗannan mutane marasa hankali ne. Idan ka duba irin mutanen da ke cikin shirin, ban san me ya shiga kawunansu ba har suka yi tunanin za su iya tinkarar rundunar soji,”

Ya kuma bayyana cewa ko da shirin ya kai ga aiwatarwa, ‘yan Najeriya da kansu za su tashi tsaye su yi adawa da shi, ganin tarihin ƙasar na gwagwarmaya da mulkin soja.

'Ba za a so juyin mulki ba,' Janar Musa

Ministan tsaron ya ce ‘yan Najeriya sun dade suna adawa da mulkin soja, yana mai tunatar da cewa Shugaba Tinubu ma na daga cikin mutanen da suka taka rawa wajen yakar mulkin soja a baya.

Ya ce yin tunanin cewa za a iya aiwatar da juyin mulki a Najeriya a wannan lokaci kuskure ne babba, yana mai cewa masu wannan tunanin suna bukatar su sake nazari.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da aka so a yi wa juyin mulki. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Juyin mulki: An kama mutum 40 a Najeriya

A wani labarin, mun kawo muku cewa Rundunar sojin Najeriya ta kama mutane akalla 40 bisa zarginsu da hannu a yunkurin juyin mulki.

Rahotanni sun nuna cewa cikin wadanda aka kama akwai manyan sojoji da ke aiki a wurare daban-daban da ma jami'an tsaron da ba sojoji ba.

Hukumomi sun kama wasu da ake zargin an hada kai da su da ba sojoji ba, kamar wani dan fim a Najeriya da direba a Aso Rock Villa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng