Sheikh Albani na So Rarara Ya ba Baban Chinedu Makudan Kudi domin Wa'azi
- Sheikh Adam Muhammad Albani ya yi kira ga mawaki Dauda Kahutu Rarara da ya taimaka wa Baban Chinedu da kudi domin shiga kauyuka wa’azi
- Malamin ya ce duk da Allah bai halatta sana’ar waka ba, Rarara yana da damar amfani da dukiyarsa wajen hidimar addinin Musulunci
- An bayyana cewa Rarara ya kasance mai taimakawa harkokin addinin Musulunci, lamarin da ya kara karfafa kiran da Sheikh Albani ya yi masa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe – Sheikh Adam Muhammad Albani Gombe ya yi kira ga Dauda Kahutu Rarara da ya taimaka wa Baban Chinedu da Adam Ashaka da kudi da motoci domin karfafa aikin da’awar Musulunci, musamman a yankunan karkara.
Sheikh Albani ya bayyana hakan ne yayin wani wa’azi da aka gudanar a masallacin Miyetti da ke unguwar Bolari a jihar Gombe, inda Baban Chinedu da Adam Ashaka suka gabatar da nasiha.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Sheikh Adam Albani ya yi game da Rarara ne a wani bidiyo da aka wallafa a shafinsa na Facebook.
Dalilin kiran Sheikh Albani ga Rarara
A cikin wa’azin, Sheikh Albani ya ce yana sane da cewa Rarara da Baban Chinedu sun taso tare a baya, kafin Baban Chinedu ya sauya akalarsa ya rungumi harkar wa’azi da koyar da addini.
Malamin ya ce wannan alaka ta baya na daga cikin dalilan da suka sa yake ganin ya dace Rarara ya taimaka masa da abokan aikinsa.
Sheikh Albani ya bayyana cewa ko da yake Allah bai halatta sana’ar waka ba, hakan ba ya hana mutum ya yi amfani da dukiyar da Allah Ya ba shi ba wajen taimakon addini.
Ya ce tallafin kudi mai yawa da kayan aiki kamar motoci zai taimaka matuka wajen bai wa malamai damar shiga kauyuka da dama domin yin wa’azi.

Kara karanta wannan
Sheikh Gumi ya gargaɗi Amurka, Isra'ila kan ƙoƙarin raba Najeriya? Gaskiya ta fito
Sheikh Albani ya bayyana cewa yana da labari game da irin ayyukan alheri da Rarara ke yi, ciki har da gina masallatai, taimaka wa marayu, da raba shinkafa da sauran kayan abinci ga talakawa.
Alaƙar Baban Chinedu da Rarara
Sheikh Albani ya ce ya tambayi Baban Chinedu kai tsaye kan irin alakar da ke tsakaninsa da Rarara, inda Baban Chinedu ya tabbatar da cewa suna da kyakkyawar alaka tun da dadewa.
Baban Chinedu ya ce sau da dama Rarara na taimaka musu da kudin man fetur idan za su yi tafiya zuwa jihohi irin su Taraba domin wa’azi.
Sai dai Albani ya bayyana cewa watakila ba a taba gabatar wa Rarara da irin wannan bukata ta musamman ta tallafin kudi mai yawa da motoci ba, shi ya sa ya yi wannan kira a fili.
Sheikh Albani ya nuna damuwarsa kan yadda malamai ke shan wahala wajen shiga kauyuka don wa’azi ba tare da samun tallafi daga masu hali ba, alhali ana ba mawaka motoci da makudan kudi.

Source: Facebook
Musulmai sun yi kira da Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa majalisar Shari'ar Muslunci ta Najeriya ta jaddada kira kan neman cire shugaban hukumar zabe ta kasa INEC, Farfesa Joash Amupitan.
Sheikh Bashir Aliyu Umar ya bayyana cewa zaman shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan a ofis hadari ne ga al'ummar Musulmi a Najeriya.
Malamin ya kara da cewa al'ummar Musulmi ba za su yarda da sakamakon zaben da Amupitan ya gudanar ba saboda halayensa da suka ce ba su dace ya shugabanci hukumar ba.
Asali: Legit.ng

