Masari Ya Ba Wa Rarara Da Baban Chinedu Kyautar Miliyan 80 Don Siyan Sabbin Gidaje

Masari Ya Ba Wa Rarara Da Baban Chinedu Kyautar Miliyan 80 Don Siyan Sabbin Gidaje

  • Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya bai wa Rarara da Baban Chinedu kyautar kudi har N80m
  • A watan Maris ne dai aka kona gidan mawaki Rarara a Kano lokacin zabubbukan gwamnoni a kasar
  • Saminu Soli a madadin kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare ya amince da fitar da kudin ga mawakan

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya sakawa mawaka biyu Dauda Kahutu Rarara da Yusuf Baban Chinedu da kudi har N80m saboda siyan sabbin gidaje.

A kwanakin baya ne wasu matasa suka konawa Rarara gida a Kano a watan Maris lokacin zaben gwamnoni a jihar.

Dauda Rarara da Baban Chinedu
Masari Ya Bai Wa Rarara da Baban Chinedu Kyautar N80m. Hoto: Channels
Asali: Twitter

Har ila yau, an kai farmaki Situdio na daukar wakokin Rarara da kuma gidan cin abinci daya mallaka, cewar TheCable.

Ma'aikatar kudi ta amince ta fitar da kudaden

Kara karanta wannan

DSS Ta Bankado Kulla-Kullan Da Wasu Ke Yi Gabannin Rantsar Da Shugaban Kasa Da Gwamnoni a Fadin Najeriya

A wata sanarwa, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta tattaro, Saminu Soli, a madadin kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar, ya amince da fitar kudaden daga asusun gwamnati.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babban akanta janar na ma’aikar kudi ya tabbatar da fitar da kudaden na N50m ga Rarara da kuma N30m ga Baban Chnedu.

An umarci ma'aikatar da gaggauta fitar da kudaden

Sanarwar ta umarci da a gaggauta aiwatar da lamarin cikin sauri ba tare da bata lokaci ba.

Sanarwar ta ce:

“Ina umartarku da fitar da kudi N80m (80,000,000) daga akanta janar zuwa ga sakataren gwamnatin jiha.
“Gwamnatin Katsina ta taimaka wa Alhaji Adamu Abdullahi Rarara da kuma Yusuf Baban Chinedu da samar musu da wurin zama da iyalansu saboda asarar da suka yi a ranar Litinin 20 ga watan Maris a Kano, kamar haka:

Kara karanta wannan

Kafin Buhari Ya Sauka Daga Mulki, An Samu Wanda Ya Maka Shugaban Kasa a Kotu

“Alhaji Dauda Adamu Abdullahi (Rarara) N50,000,000.00 (N50m) da kuma Baban Chinedu N30,000,000.00, ()N30m, jimilla N80,000,000.00. (N80m)."

Wannan tausayawa na gwamnan na zuwa ne kasa da mako daya kafin ya sauka daga karagar mulki.

Rarara da Baban Chinedu sun shahara wurin yi wakokin jam’iyyar APC ta kasa da kuma jihar Kano musamman a lokutan gangamin yakin neman zabe.

Mawaki Rarara Ya Nemi Kotu Tayi Watsi Da Karar Da Ake Masa

A wani labarin, mawaki Kahutu Rarara ya roki kotun shari'ar Musulunci ta yi watsi da karar da aka shigar gabanta akansa.

Shahararren mawakin ya bukaci kotun da yin fatalin ne bayan an kai kararsa da kin biyan dan kasuwa kudadensa da suka kai N10m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel