Sojoji Sun Yi Lalata da Mata, Sun Tatsi Talakawa a Cross River? Gaskiya Ta Fito
- Rundunar sojoji ta 13 Brigade ta musanta zargin fyade da karbar kudin jama'a da ake yi wa dakarunta a lokacin rikicin Alesi da Ochon
- Binciken sojoji ya nuna cewa bidiyon dake yawo a yanar gizo karya ne kuma an shirya shi ne domin bata sunan rundunar soja a idon jama'a
- Rundunar ta fada wa mazauna Cross Rivers matakin da za su iya dauka don mika koke-kokensu idan har akwai wani soja da ya ci zarafinsu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rundunar sojin Najeriya, musamman shalkatar runduna ta 13 (13 Brigade), ta musanta wasu zarge-zarge da ke yawo a kafafen sada zumunta game da dakarunta.
Rundunar ta musanta zargin cewa dakarunta sun yi wa mata fyaɗe tare da karɓar kuɗin talakawa a lokacin rikicin ƙabilanci tsakanin Alesi da Ochon a jihar Cross River.

Source: Twitter
Sojoji sun ci zarafin mata a Cross Rivers?
Mataimakin daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, Manjo Yemi Sokoya, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, 30 ga Janairu, 2026, in ji rahoton Punch.
Sanarwar ta bayyana cewa waɗannan zarge-zarge, waɗanda aka yaɗa a wani bidiyo dake magana kan abubuwan da suka faru tun watan Satumban 2025, ƙarya ne tsantsa kuma ba su da tushe balle makama.
Bayan yaɗuwar bidiyon, rundunar sojin ta ƙaddamar da binciken gaggawa ta hanyar jami'an tsaron soja domin gano gaskiyar lamarin.
A karshen binciken, eundunar ta ce bincikenta ya nuna babu wani soja da ya ci zarafin mata ko yi masu fyaɗe. Haka kuma, ba a samu shaidar cewa sojoji sun tatsi kuɗi ko kwashe kayan jama'a ba.
Shirga ƙarya domin ɓata sunan soja
Major Sokoya ya jaddada cewa dakarun sojin sun yi aiki ne ƙarƙashin tsauraran dokoki domin maido da zaman lafiya, kuma rundunar ba ta wasa da batun keta haƙƙin bil'adama.

Kara karanta wannan
Birgediya Janar Sadiq: Bayanan da muka sani kan sojan da ake zargi da hannu a 'juyin mulki'
Rundunar ta bayyana cewa waɗannan zarge-zarge an shirya su ne da gangan domin ɓata sunan dakarun soji da kuma hana samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankunan Alesi da Ochon.
Sanarwar ta yi nuni da wani rahoto na ɗan jarida mai bincike, Efio Ita, wanda aka wallafa a ranar 24 ga Satumba, 2025, wanda ya nuna cewa an shirya bidiyon ne domin rage wa sojoji kwarjini a idon jama'a.

Source: Original
Gargaɗi ga masu yaɗa jita-jita
Ya zuwa yanzu, babu wani mutum da ya shigar da ƙara a hukumance tare da bayar da rahoton likita ko shaidar ƴan sanda da za su nuna cewa an aikata waɗannan laifuka a kansa.
Rundunar sojin ta gargaɗi jama'a da su daina yaɗa rahotannin da ba su tabbatar da gaskiyarsu ba, domin hakan na iya rura wutar rikici tsakanin al'umma.
Ta kuma buƙaci dukkan wanda yake da korafi na gaskiya da ya bi hanyoyin da suka dace na shari'a ko na rundunar soja domin shigar da ƙara maimakon yin amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa ƙarya.
Ana kama sojoji kan cin zarafin farar hula
A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu jami'an rundunar sojin kasar nan sun fusata shugabanninsu bayan an gano su na cin zarafin wani farar hula a Legas.
Wannan na zuwa ne bayan an dauki sojojin a bidiyo, inda aka rika ganin yadda sojojin su ka ci zarafin farar hula guda biyu a Badagry, Legas.
Rundunar sojojin Najeriya dai ta bayar da hakuri ga jama'ar da lamarin ya fusata, ta kara da cewa bincike ya yi nisa domin gano musabbabin abin da ya faru.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

