Yadda Sojojin Najeriya da Sojojin Kamaru suke cin zarafin yan Mata da Mata a sansanin yan gudun hijira
Wasu yan mata mazauna sansanin yan gudun hijira dake jihar Borno sun bayyana ma Duniya yadda dakarun Sojojin Najeriya da na kasar Kamaru ke musu fyade suna cin zarafinsu kafin su basu abinci su ci, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan matan sun bayyana haka ne a ranar Alhamis 24 ga watan Mayu, a yayin taron da kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta shirya a garin Abuja, inda suka bayyana rahoton cin zarafi da Sojoji ke yi a sansanin yan gudun hijira.
KU KARANTA: Bahallatsar Shekarau da EFCC: Rashin adalcin Buhari ne – Inji magoya baya
Majiyar ta ruwaito matsalar ta kai ga har Sojoji suna hana yan mata abinci, har sai sun basu kansu sun yi amfani dasu sa’annan zasu basu abincin, sakamakon matsananciyar yunwa da ake fama da ita a can.
Guda daga cikin yan matan, Kella Haruna ta bayyana cewa bama Sojoji kadai ba, hatta Sojojin sa kai na Sibiliyan JTF ma suna neman yan matan dake sansanin, kuma idan basu basu hadin kai ba, zasu tsangwamesu su sa musu iido.
Kella ya kara da cewa tana sane dsa cewa da ace mazajensu suna raye da duk ba zasu fuskanci wulakancin nan ba, sa’annan tace: “Sojoji ne suka kwashe mazajenmu suka rufe musu idanu suka tafi dasu zuwa wani wuri da har yanzu basu sake ganinsu ba, daga baya kuma suka dawo suka kwashe mu da nufin zasu kaimu wajen mazajenmu, amma sai suka jibge mu a sansanin yan gudun hijira dake Bama.
“A gaskiya a sansanin Bama bamu samun ruwa, babu abinci, kuma idan muka yi korafi sai a buge mu,haka zalika Sojoji sun kwace mana kudadenmu.” Inji ta. Ita ma wata mata mai suna Fatima Bukar ta ce har yanzu bata samu labarin mijinta da danta ba, kuma Sojoji ne suka kama su.
Dayake tsokaci game da rahoton, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa kamata yayi gwamnati ta bincike gaskiyar rahoton Amnesty International.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng