Gwamnatin Tinubu Ta Ware Gidajen Talakawa Miliyan 15 da Za Ta Ba Tallafin Kudi
- Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa shirin tallafin kudi ya isa ga gidaje miliyan takwas wadanda ke dauke da 'yan Najeriya miliyan 35
- Minista Bernard Doro ya sanar da shirin fadada tallafin kudin zuwa gidaje miliyan 12 a fadin kasar nan domin rage radadin talauci
- An gudanar da taron ne a Calabar inda aka tattauna yadda za a hada kan dukkan shirye-shiryen tallafi domin taimaka wa marasa karfi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Calabar - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa shirin ta na bayar da tallafin kuɗi (CCT) ya isa ga gidaje sama da miliyan 8.3, inda ya taimaka wa ƴan Najeriya fiye da miliyan 35 zuwa yanzu.
Ministan jin ƙai da rage talauci, Dr. Bernard Doro, ne ya bayyana hakan a babban taron ƙasa na farko kan harkokin jin ƙai da aka gudanar a garin Calabar, Jihar Cross River, tsakanin 27 zuwa 29 ga watan Janairu, 2026.

Source: Twitter
Muhimmancin tallafin CCT ga talaka
Dr. Doro ya ce gwamnati tana da shirin faɗaɗa wannan tallafi domin ya isa ga gidaje miliyan 15 a faɗin ƙasar nan nan da wani ɗan lokaci, domin ceto miliyoyin mutane daga ƙangin talauci, in ji rahoton The Guardian.
Ministan ya jaddada cewa shirin CCT, wanda ke amfani da rajistar NSR, shi ne babban ginshikin da gwamnati ke amfani da shi wajen rage raɗaɗin talauci da samar da hanyoyin dogaro da kai ga marasa ƙarfi.
A cewarsa, ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta kamar rashin tsaro, sauyin yanayi, da matsin tattalin arziki sun sa ya zama dole a samar da tsari guda ɗaya na ƙasa maimakon gudanar da ayyuka daban-daban ba tare da haɗin kai ba.
Manufar "tsarin jin ƙai na bai ɗaya"
Ministan ya bayyana cewa sabuwar majalisar da aka ƙaddamar za ta yi aiki wajen haɗa dukkan shirye-shiryen tallafi wuri guda domin kauce wa maimaita ayyuka da kuma tabbatar da cewa kuɗaɗen tallafi sun isa inda ake buƙata.
Hukumomin da ke ƙarƙashin ma'aikatar, kamar hukumar kula da ƴan gudun hijira, hukumar kula da nakasassu, da kuma cibiyar kula da tsofaffi, duka za su haɗa kai wajen aiwatar da wannan manufa ta Shugaba Bola Tinubu.

Source: UGC
Goyon baya daga matakin jihohi
Gwamnan Cross River, Bassey Otu, wanda ya karɓi baƙuncin taron, ya yaba wa gwamnatin tarayya kan ba da fifiko ga rage talauci, in ji rahoton Punch.
Gwamnan ya koka kan yadda jiharsa ke fama da ƴan gudun hijira daga Kamaru kusan 50,000 da kuma matsalar ambaliyar ruwa.
Gwamnan ya yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin magance waɗannan matsaloli dake addabar al'ummar karkara.
Shettima ya kaddamar da shirin tallafin N1bn
A wani labari, mun ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kaddamar da shirin tallafin kasuwanci ga ƙananan yan kasuwa.
Shettima ya ce tsarin tallafin iyali zai ƙara yawan sana’o’i, ya bunƙasa kuɗaɗen shiga, ya ƙarfafa matasa da mata, tare da rage dogaro da wasu.
Ya shawarci masu cin gajiyar su yi amfani da jarin yadda ya kamata, saboda yana da damar haifar da ci gaban zuri’a inda ya ce za a ɗauki kowa a matakai na gaba.
Asali: Legit.ng

