Garba Shehu: Dalilan da Suka Jawo Buhari Ya Kori Hadiza Bala Usman duk da Kusancinsu

Garba Shehu: Dalilan da Suka Jawo Buhari Ya Kori Hadiza Bala Usman duk da Kusancinsu

  • Hadimin tsohon Shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana dalilin da ya sa marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Hadiza Bala Usman
  • Ya ce Marigayi Buhari ya yi watsi da alakar da ke tsakaninsa da Hadiza Bala wurin korar da daga shugabancin hukumar NPA saboda wasu dalilai
  • Garba Shehu ya ce shawarar dakatarwar ta fito ne daga tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi a wancan lokaci yayin da ita ta ke kula da tasohin ruwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Garba Shehu, ya bayyana yadda aka kori Hadiza Bala Usman daga shugabancin NPA.

Ya ce marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Hadiza Bala Usman daga hukumar tashoshin jiragen ruwa ta (NPA) ne bisa shawarar da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Ganduje ya tura wa Kwankwaso goron gayyatar sulhu

Garba Shehu ya fadi dalilin Buhari na korar Hadiza Usman
Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi tare da Hadiza Usman Hoto: Hadiza Usman/Rotimi Amaechi
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Garba Shehu ya ce duk da kusancin da ke tsakanin Buhari da Hadiza Bala Usman, wanda ya kai matsayin 'ya da uba, bai hana korarta ba.

A wancan lokaci, NPA na daga cikin hukumomin da ke ƙarƙashin kulawar Amaechi daga shekarar 2015 zuwa 2022.

Amaechi ya yi silar korar Hadiza Bala Usman

Garba Shehu ya ce a cewar Amaechi, an bayar da shawarar dakatar da Hadiza Bala Usman ne sakamakon zargin cewa hukumar NPA ta kasa mayar da N165bn na ribar aiki cikin asusun gwamnatin tarayya.

Wannan zargi ne ya haifar da rikici mai zafi a tsakanin shugabannin gwamnati a lokacin, har ta aka kai ga bayar da shawarar a sallame ta.

Garba Shehu ya ce Buhari ya bi ka'ida wajen aikinsa
Garba Shehu, hadimin tsohon Shugaban kasa yana zuba jawabi Hoto: Garba Shehu
Source: Twitter

Sai dai daga baya, an kafa wani kwamitin bincike na gudanarwa domin duba batun, wanda ya wanke Hadiza Bala Usman daga dukkanin zarge-zargen almubazzaranci da aka yi mata.

Kara karanta wannan

Sai Tinubu: 'Dan Atiku ya sha alwashi, za a hadu da shi a kada mahaifinsa a 2027

A halin yanzu, Hadiza Bala Usman na aiki a matsayin mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara ta musamman kan manufofi da haɗin gwiwar gwamnati.

Abin da Garba Shehu ya ce game da Buhari

Da yake magana a Abuja yayin tattauna sabon littafinsa mai suna 'According to the President', Garba Shehu ya ce lamarin Hadiza Bala Usman ya nuna irin salon shugabanci da Muhammadu Buhari ke da shi.

Ya ce Buhari ya karɓi wasiƙa daga Amaechi inda ya nemi a dakatar da Hadiza Bala Usman daga aiki.

Duk da cewa akwai rashin jituwa tsakanin ministan da shugabar NPA a lokacin, shugaban ƙasa ya tsaya kan tsarin mulki da ikon da ke hannun ministan da ke kula da hukumar.

A cewar Garba Shehu, babban hafsan shugaban ƙasa ya yi ƙoƙarin shawo kan Buhari da cewa bai kamata a dakatar da Hadiza ba.

Sai dai Buhari ya nace cewa minista ne ke kula da ita kai tsaye, kuma idan ya yanke hukuncin cewa ba ta dace da muƙamin ba, to dole ne a aiwatar.

Kara karanta wannan

Shugaban hukumar alhazai ya hakura da gwamnatin Abba, ya yi murabus

Garba Shehu ya ƙara da cewa wannan lamari ya nuna cewa Buhari mutum ne da ba ya barin sha’anin ƙasa ya gauraya da alaƙar da ke tsakaninsa da mutum.

Hadiza Bala Usman ta shiga daga ciki

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban ma'aikatan fadar Shugaban kasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya yi jawabi mai cike da yabo da girmamawa ga Hajiya Hadiza Bala Usman.

Hajiya Hadiza Bala Usman, ita ce ke riƙe da muƙamin mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara ta musamman kan daidaita manufofi da ayyukan gwamnati.

Gbajabiamila ya bayyana hakan ne a babban taron murnar cikar Hadiza Bala Usman shekara 50 da haihuwa, tare da korafin an sha bikinta ba tare da gayyata ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng