Saudiyya Za Ta Ɗauki Ƴan Najeriya Aiki, an Faɗi Fannonin da Za a Jefa Su a Ƙasar
- Ƙasar Saudiyya ta amince da ɗaukar ’yan Najeriya aiki a hukumance bayan yarjejeniya da aka ƙulla domin tsara daukar ma’aikata da kare hakkokinsu
- Yarjejeniyar na cikin manufofin 'Vision 2030' da Saudiyya ke aiwatarwa domin gyaran tsarin aiki da bunƙasa tattalin arzikinta
- Najeriya na ganin yarjejeniyar a matsayin dama mai muhimmanci wajen rage rashin aikin yi, tare da tabbatar da kariya da walwalar ’yan ƙasar a waje
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Riyadh, Saudiyya - Kasar Saudiyya ta bayyana shirinta na ɗaukar ’yan Najeriya aiki yayin da ake fama da matsalar rashin aikin yi musamman a tsakanin matasa.
Saudiyya za ta dauki aikin ne bayan wata sabuwar yarjejeniya da aka cimma tsakanin gwamnatocin ƙasashen biyu da ke da kyakkyawar alaka.

Source: Facebook
Najeriya ta rattaba hannu a yarjejeniya da Saudiyya
Hakan na cikin wata sanarwa da shafin ma'aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta tabbatar a manhajar Facebook a jiya Alhamis 29 ga watan Janairun 2026.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne tsakanin Ministan Ci gaban Jama’a na Saudiyya, Injiniya Ahmed bin Sulaiman Al-Rajhi, da Ministan Kwadago da samar da ayyukan yi na Najeriya, Dakta Muhammad Maigari Dingyadi.
Yarjejeniyar ta mayar da hankali ne kan tsarin ɗaukar ma’aikata cikin gaskiya da bin doka, tare da tabbatar da walwala da tsaron rayuwar ma’aikatan Najeriya.
Haka kuma, an bayyana cewa nan ba da jimawa ba hukumomin da abin ya shafa za su fitar da sharuɗɗa da ƙa’idojin da dole masu neman aikin su cika domin samun wannan dama.
Matakin na daga cikin shirin 'Vision 2030' na Saudiyya, wanda ke da burin sabunta tattalin arziƙi da rage dogaro da man fetur kaɗai a kasar.

Source: Facebook
Fannonin da ake bukatar samar da aikin
A halin yanzu, Saudiyya na buƙatar ƙarin ma’aikata a fannoni irin su gine-gine, kiwon lafiya, otal-otal, sufuri da ayyukan hidima wanda zai rage rashin ayyuka a Najeriya.
Duk da cewa a baya ƙasashen Asiya ne suka fi mamaye ayyuka a Saudiyya, yanzu ƙasashen Afirka, musamman Najeriya, na samun karɓuwa a gurabe da dama a kasar.
Ga Najeriya, wannan yarjejeniya na zuwa ne a daidai lokacin da rashin aikin yi ke ƙara ta’azzara, musamman a tsakanin matasa masu neman damar aiki a gurabe da daya.
Gwamnati na fatan tsarin zai taimaka wajen kare haƙƙin ’yan Najeriya a ƙasashen waje, tare da ƙara kudaden shiga ga tattalin arziƙin ƙasa.
Gwamnati za ta magance matsalar rashin aiki
Kun ji cewa matsalar rashin aikin yi ta daɗe tana ci wa mutanen Najeriya musamman matasa waɗanda ke zaman kashe wando tuwo a ƙwarya.
Ministan ƙwadago da samar da ayyuƙan yi, Muhammadu Dingyadi, ya bayyana cewa gwamnati ta duƙufa wajen ganin ta magance matsalar.
Ya bayyana cewa an ƙirƙiro shirye-shiryen koyar da sana'o'i domin ganin matasa sun samu abin yi, ta yadda za su iya dogaro da kansu.
Asali: Legit.ng

