Kasar Amurka Ta ba 'Yan Najeriya Damar Yin Karatu Kyauta

Kasar Amurka Ta ba 'Yan Najeriya Damar Yin Karatu Kyauta

  • Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya sanar da fara kwasa-kwasan koyon Turanci kyauta domin ƙara ƙwarewar sana’a da faɗaɗa damar samun aiki
  • An tsara kwasa-kwasan ne ta shirin OPEN na ma’aikatar harkokin wajen Amurka, inda mahalarta za su koyi darussa tare da hulɗa da masu koyo daga ƙasashe
  • Rahotanni sun nuna cewa za a fara gudanar da darusan daga ranar 5, Janairu, 2026 zuwa 30, Maris, 2026, tare da buɗe rajista har zuwa 23, Maris, 2026

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya sanar da ƙaddamar da wasu kwasa-kwasan koyon Turanci kyauta ta yanar gizo, waɗanda aka tsara domin taimaka wa masu koyo su bunƙasa ƙwarewar sana’a.

Haka zalika an bayyana cewa shirin zai ba mutane daga kasashe fadada damar samun ayyukan yi a fannoni daban-daban a duniya.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An fallasa yadda aka shirya kashe Tinubu, Shettima da wasu mutum 2

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump da wani aji ana koyar da karatu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sanarwar ta fito ne a wani saƙo da ofishin ya wallafa a shafinsa na X, inda ya bayyana cewa shirin na da nufin tallafa wa jama'a.

Manufar kwasa-kwasan Amurka

A cewar ofishin jakadancin Amurka, an tsara kwasa-kwasan ne domin ƙarfafa basirar sadarwa da ake buƙata sosai a wuraren aiki na zamani.

Punch ta rahoto cewa shirin yana karkashin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta hanyar Online Professional English Network, wato OPEN.

Abubuwan da za a koyar da mutane

Rahoto ya nuna cewa akwai kwasa-kwasa da dama da aka tanada a wannan zagaye domin jama'a su samu damar bunkasa rayuwarsu.

Daga ciki har da “English for Business and Entrepreneurship,” wanda aka tsara domin haɓaka kasuwanci da kuma inganta dabarun sadarwa a harkokin kasuwanci.

Haka kuma akwai “English for Tourism Professionals,” wanda ya dace da mutanen da ke aiki ko ke sha’awar aiki a fannoni kamar tafiye-tafiye, yawon buɗe ido da otal-otal.

Kara karanta wannan

Matashin da ya mallaki bindiga a Kano ya yi wa mahaifiyarsa dukan tsiya

Wani kwas ɗin kuma shi ne “English for Career Development,” inda mahalarta za su koyi yadda ake rubuta takardun neman aiki masu ƙyau, yadda ake neman aiki, da kuma yadda za a tattauna da masu bayar da aiki.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump
Donald Trump na yi wa mutane jawabi a taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yadda za a yi jarista a fara karatu

Ofishin jakadancin Amurka ya ce za a fara gudanar da kwasa-kwasan ne daga 5, Janairu, 2026, kuma za su ƙare a ranar 30, Maris, 2026. An buɗe rajista tun daga 5, Janairu, 2026, kuma za a rufe ta a ranar 23, Maris, 2026.

A cewarsa, masu sha’awa za su iya yin rajista ta hanyar dandalin koyon karatu na yanar gizon shirin, inda za su samu cikakken bayani kan yadda za su shiga a nan.

Ana zanga-zanga a kasar Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa matasa na kara fitowa kan tituna a kasar Amurka suna zanga-zangar adawa da jami'an shige da fice.

Zanga-zangar ta kara kamari ne a jihohi da dama bayan jami'an ICE sun harbi wani matashi da ya kasance ma'aikacin lafiya a kasar.

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana shirin duba matakin da zai dauka, yayin da gwamnatin kasar ta kare jami'in da ya yi harbin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng