Jerin Kasuwanci 7 da Zasu Samar da Miloniyoyi a Afrika a 2022

Jerin Kasuwanci 7 da Zasu Samar da Miloniyoyi a Afrika a 2022

  • Damammakin habaka kasuwanci a Afrika da najeriya a koda yaushe kara yawaita yake yi sakamakon yawan jama'a dake karuwa
  • An yi kiyasin cewa, 'yan Najeriya 16.7 ne zasu shiga matsalar abinci wanda zai bada damar habakar kasuwanci a wannan bangaren
  • Hakazalika, masana'anatar kyale-kaye tana cigaba da habaka tare da sauyawa zuwa kasuncin biliyoyin daloli a Afrika inda ta kai darajar $4 biliyan

Ga wasu jerin masana'atun bakwai da zasu samar da miloniyoyi a Najeriya da nahiyar Afrika baki daya a 2022.

Masana'antar yada labarai da nishadantawar

Kamar yadda rahoton kwanan ya bayyana, fasaha ta taka rawar gani a masa'antar nishadi a Afrika kuma ta sauya ta daga nishadi zuwa wurin samun biliyoyin daloli.

Kiyasi ya bayyana cewa, kudin da ake samu a fannin nishadi a Afrika ya kai $32.19 miliyan a 2022.

Kara karanta wannan

Manyan 'Yan Ta'adda 8 Sun Shiga Hannun Dogaran Fadar Shugaban Kasa a Abuja

Bugu da kari, ana tsammanin dukkan kudin da ake samu a kowacce shekara zai karu da kashi 8.02 inda za a kai $43.83 miliyan zuwa 2026.

Millionaires
Jerin Kasuwanci 7 da Zasu Samar da Miloniyoyi a Afrika a 2022. Hoto daga Peathegee Inc
Asali: Getty Images

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abinci da kasuwancin kayan gona

Kamar yadda binciken kwanan nan ya bayyana, a Najeriya abinci da kayyaykin da suka shafe shi a kasuwa suna da kudin shiga da ya kai $45,7 biliyan a 2022 wanda ke bayyana cigaban kashi 5.8 tsakanin 2016 zuwa 2020 inda kudin shigar jimillarsa ya kai $35.1 biliyan.

'Yan kasuwar abinci da masu kasuwancin kayan gona ana sa ran su zama miloniyoyi kafin karewar 2022.

Kyale-kyale da kwalliya

Masana'antar kyale-kyale da kwalliya a koda yaushe cigaba take kuma jimillar kudin da take samu ya kai $4.80 biliyan a shekara.

A 2020, bincike ya nuna cewa wannan kasucin a Najeriya yana da darajar $4.8 biliyan kuma yana samun cigaba da 5.5% kuma ana sa ran za a samu kari zuwa $6.3% zuwa 2022.

Kara karanta wannan

Osinbajo, Lawan, Da Sauran Mutum 20 Da Suka Sayi Fom Din APC Zasu Gana Don Tinubu

Dillancin gidaje da filaye

Rahoton GDP da NBS ta fitar yace fannin kasuwar dillanci ta samu cigaba da kashi 1.77 inda ta bada gudumawar 5.28% na GDP a Najeriya a 2021 wanda ya kai ga $5.3 biliyan.

Intanet da Fasaha

Hukumar Kudi ta Duniya tace ma'abota amfani da intanet a Afrika kuma suke da sani a fannin fasaha suna karuwa a nahiyar.

A kowacce shekara na samun karin kashi 10 na samu samun damar amfani a Intanet a Afrika duk da a halin yanzu akwai 40%.

Harkokin kudi na zamani

Bankin duniya yace 'yan Afrika da basu iya samun harkokin kudi na zamani suna harkokin kasuwancinsu ne ta hanyar amfani da kudi tsabarsu.

Hanyoyin harkar kudi kamar Flutterwave, Paystack da sauransu suna da darajar sama da $1 biliyan kuma ana sa ran cigabansu nan da 2025.

Cinikayya ta kasuwanci

Statista tace a 2020, kashi bakwai na cinikyayya a Najeriya ana yin su ne a yanar gzio. Cinikayya ta yanar gizo tana da kashi mai tsoka a tsakanin kasashen Afrika biyar. Akwai Misra, Afrika ta Kudi, Kenya da Morocco.

Kara karanta wannan

Magidanci Mai Mata 4 Da 'Yaya 34 Sun yi Rijistan Zabe, Yace Atiku Duk Zasu Kadawa Kuri'u

Hakan yasa ake hango samun miloniyoyi a banfaren kafin karewar 2022.

'Dan Biloniya BUA Yayi Murabus Daga Kasuwancin Mahaifinsa, Kasa da Shekara 1 da Zama ED

A wani labari na daban, 'dan biloniyan 'dan kasuwa, Rabiu Abdulsamad Rabiu, ya yi murabus daga matsayin zababben daraktan kamfanin BUA Foods Plc, daya daga cikin manyan kamfanonin samar da abinci a kasar nan.

Naziru ya bar kamfanin mahaifinsa tun daga ranar 17 ga watan Augustan 2022 kamar yadda takardar da kamfanin ya fitar ta bayyana.

Matashi Naziru bai bayyana dalilinsa na yin murabus kwatsa ba. Har ila yau, wani bangare na takardar da kamfanin ta fitar ga Hukumar Tsaro da Musaya ta Najeriya tace murabus dinsa ya fara aiki daga ranar 17 ga watan Augusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel