Halin da Marasa Lafiya Suka Shiga da Aka Rufe Asibitoci a Birnin Tarayya Abuja
- Marasa lafiya sun shiga garari sakamakon yajin aikin kungiyar JUAC wanda ya jawo janyewar likitoci daga asibitocin gwamnati a Abuja
- Ma'aikatan Abuja karkashin jagorancin Femi Falana sun daukaka kara kan hukuncin kotun masana'antu da ya umarce su da su koma aiki
- Minista Nyesom Wike ya yi barazanar daukar mataki kan duk ma'aikacin da ya ki komawa bakin aiki yayin da yajin aikin ke kara tsananta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Marasa lafiya dake neman magani a kananu (PHCs) da manyan asibitocin gwamnati a Abuja sun tsinci kansu cikin mawuyacin hali a ranar Laraba.
Wannan kuwa ya faru ne sakamakon fadada yajin aikin da mambobin hadakar kungiyoyin ma’aikatan babban birnin tarayya (JUAC) suka yi.

Source: UGC
Asibitoci da makarantu sun koma kufai
Wannan yajin aiki, wanda ya fara tun ranar Litinin din da ta gabata, ya samo asali ne daga zargin "cin amanar ma'aikata" da "rashin daukar mataki" kan korafe-korafen ma'aikata da gwamnatin birnin tarayya (FCTA) ta yi, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan
'Sun san da zuwan mu,' Yadda aka kashe babban sojan Najeriya da jami'ai 9 a Borno
Binciken da manema labarai suka gudanar ya nuna cewa asibitoci da dama sun kasance tamkar kufai, inda aka ga 'yan tsirarun marasa lafiya suna rika jiran tsawon sa'o'i ba tare da ganin ma'aikaci ko daya ba.
Wata marar lafiya a asibitin Abaji, Mrs. Grace Yohana, ta bayyana cewa:
"Na zo duba lafiya ta ne amma aka ce min ma'aikata na yajin aiki. Dole na koma gida na nemi wani asibitin kudi."
Fannonin da yajin aiki ya shafa a Abuja
Shi ma Mista Ibrahim Saleh ya koka kan yadda ya kasa samun ganin likita ko magani mai rahusa yayin da ya ce yana fama da rashin wadatar zuwa asibitin kudi.
Baya ga fannin lafiya, yajin aikin ya shafi:
- Makarantu: An rufe makarantun Firamare da na sakandaren gwamnati a dukkan kananan hukumomi shida na Abuja.
- Hukumomi: An rufe dukkan gine-ginen hukumar filaye (AGIS), hukumar tsaftar muhalli (AEPB), da hukumar samar da ruwan sha (FCT Water Board).
Ma'aikata sun kalubalanci hukuncin kotu
A daidai lokacin da ministan Abuja, Nyesom Wike, ya samu nasara a gaban kotun masana'antu inda aka ba ma'aikata umarni su koma bakin aiki, kungiyar JUAC ta ki bin wannan umarni.

Source: Facebook
Nyesom Wike ya yi barazana cewa dukkan ma'aikacin da ya ki komawa bakin aiki zai fuskanci sakamako mai tsanani, in ji rahoton Punch.
Sai dai kungiyar JUAC, karkashin jagorancin lauyan nan mai fafutukar kare hakkin bil'adama, Femi Falana (SAN), ta daukaka kara kan wannan hukunci a ranar Laraba. Ma'aikatan sun dage cewa ba za su koma aiki ba har sai an biya musu bukatunsu.
Wannan takun-saka tsakanin ma'aikata da gwamnati ya sanya mazauna kauyuka kamar Kwaku da Yebu tafiya mai nisa zuwa cikin birnin Abuja domin neman magani a asibitoci masu zaman kansu masu tsada, wanda hakan ke kara jefa talaka cikin talauci.
Kotu ta jikawa likitoci aiki a Abuja
Tun da fari, mun ruwaito cewa, babbar kotun masana'antu dake Abuja ta dakatar da kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki daga shiga yajin aiki.
Mai shari'a E. D. Subilim ya bayar da wannan umarni ne bayan gwamnatin tarayya ta shigar da korafi domin hana likitocin janye ayyukansu na duba marasa lafiya.
Likitocin da ke neman kwarewar aiki sun yi barazanar fara yajin aikin ne saboda zargin rashin gaskiyar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a bara.
Asali: Legit.ng
