'Sun San da Zuwan Mu,' Yadda Aka Kashe Babban Sojan Najeriya da Jami'ai 9 a Borno

'Sun San da Zuwan Mu,' Yadda Aka Kashe Babban Sojan Najeriya da Jami'ai 9 a Borno

  • Sojojin Najeriya sun gano gawarwakin wani kwamandan bataliya da wasu dakaru tara wadanda 'yan ta'addan Boko Haram suka kashe
  • 'Yan ta'addan sun yi wa sojojin kwanton-bauna ne a tsakanin Damasak da Geidam lokacin da dakarun ke hanyar tunkarar sansaninsu
  • Jiragen yakin dakarun sama sun taimaka wajen fatattakar 'yan ta'addan da suka boye domin jiran sojoji su zo kwashe gawarwakin dakarun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Dakarun sojoji Najeriya sun yi nasarar dauko gawarwakin wani kwamandan bataliya, wani Manjo, da sauran sojojin da mayakan Boko Haram suka kashe a yankin Damasak dake jihar Borno.

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa mayakan sun kashe sojoji bakwai tare da yin garkuwa da kwamandan da wasu sojoji 12 yayin wani hari da suka kai ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Yadda aka kama kayan hada bama bamai masu yawa za a kai wa ƴan bindiga a Zamfara

'Yan ta'addan Boko Haram sun kashe babban sojan Najeriya da wasu dakaru.
Sojojin Najeriya suna a bakin aiki. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

An gano gawarwakin sojoji a Borno

Sai dai, majiyoyin tsaro sun tabbatar wa jaridar Daily Trust cewa 'yan ta'addan sun kashe kwamandan, sojoji bakwai, da mambobin rundunar sa-kai (CJTF) guda biyu bayan sun kamo su.

Wata majiya ta bayyana cewa an gano gawarwakin ne a ranar Laraba, bayan wani gagarumin fafatawa da sojojin ƙasa suka yi, tare da tallafin jiragen yaƙi na dakarun sama.

Majiyar ta ce:

"Da farko mun yi tunanin an kama kwamandan ne da ransa, amma daga baya aka gano cewa an kashe shi tare da sauran. An ɗaure hannayensu aka harbe su, wasu gawarwakin kuma an jefa su a ruwa."

Tarkon da aka dana wa sojojin a Borno

Bayan kashe sojojin, 'yan ta'addan sun ɓuya a cikin daji domin jiran dakarun ceto, amma sojoji sun fatattake su tare da taimakon jiragen yaƙi kafin su kwashe gawarwakin zuwa Maiduguri.

Rundunar sojojin tana kan hanyar tunkarar wani babban sansanin 'yan ta'adda dake tsakanin Damasak da Geidam ne lokacin da aka yi musu kwanton-ɓauna.

Kara karanta wannan

Shiri ya baci: 'Yan Boko Haram sun kashe sojoji, sun cafke wani babban soja a Borno

"Ya nuna cewa sun riga sun samu labarin shirinmu, sun san da zuwan mu, domin sun kewaye mu a kan hanya sannan suka buɗe mana wuta ta kowane ɓangare," in ji majiyar.
An ce sojoji sun fada tarkon 'yan ta'addar Boko Haram ne a yankin Damasak
Taswirar jihar Borno, inda Boko Haram ta hallaka akalla sojoji 8 da CJTF 2. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji sun tsananta hare-hare

A halin yanzu, rundunar sojin Najeriya ta tsananta kai hare-hare a yankunan dajin Sambisa, duwatsun Mandara, da yankin Tafkin Chadi domin ragargazar ragowar 'yan ta'addan.

Duk da wannan babban rashi, sojoji sun samu nasarori da dama a kwanan nan, inda suka tarwatsa sansanonin Boko Haram da ISWAP tare da kashe manyan kwamandojinsu.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar sojin ƙasa ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba, kuma har yanzu ana jiran martani daga bakin kakakinta.

Sojoji sun kutsa sansanin Boko Haram

A wani labari, mun ruwaito cewa, Rundunar sojoji ta samu nasara bayan kutsawa cikin yankin Timbuktu Triangle, wani yanki da ake dangantawa da Boko Haram da ISWAP.

A yayin ci gaba da kakkabe ‘yan ta’adda, sojoji sun yi artabu da mayakan kungiyar Boko Haram, lamarin da ya janyo asara ga dukkan bangarorin biyu.

Rundunar ta ce an gano kaburburan ‘yan ta’adda da dama, abin da ke nuna irin mummunan raunin da aka yi musu a wadannan hare-hare da aka kai kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com