Uba Sani da Tsofaffin Sanatocin da Ke Rike da Mukaman Gwamonin Jihohi Yau a Najeriya

Uba Sani da Tsofaffin Sanatocin da Ke Rike da Mukaman Gwamonin Jihohi Yau a Najeriya

FCT, Abuja - Najeriya na da gwamnoni 36 wadanda ke mulki a jihohinsu bayan sun samu nasara a zabubbukan da hukumar INEC ta shirya.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Wasu daga cikin wadannan gwamnonin sun wakilci mazabunsu a matsayin sanatoci na majalisar dattawa kafin su hau kujerar gwamna.

Wasu tsofaffin sanatoci na rike da mukamin gwamna
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Hoto: Senator Uba Sani, HE Sen Monday Okpebholo, Bala Abdulkadir Mohammed
Source: Facebook

Legit Hausa ta zakulo gwamnonin da ke kan mulki a yanzu wadanda suka kasance tsofaffin sanatoci a majalisar dattawa.

Sanatocin da suka dare kujerar gwamna

Galibi a fagen siyasar Najeriya an fi samun gwamnonin da ke zama sanatoci bayan sun kammala wa'adinsu na mulki.

Sai dai, wasu tsofaffin sanatoci na zama gwamnoni bayan sun wakilci mazabunsu a majalisar dattawan Najeriya.

A yanzu haka, akwai tsofaffin sanatoci da suka yi zama a majalisar dattawa guda bakwai da ke kan kujerar gwamna a jihohinsu.

Ke jerin gwamnonin da suka taba zama sanatoci a baya:

Kara karanta wannan

Wasu kwamishinoni sun rikita gwamnatin Kano bayan komawar Abba APC? Gaskiya ta fito

1. Bala Mohammed (jihar Bauchi)

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed na cikin jerin tsofaffin sanatocin da ke rike da mukamin gwamna a jihohinsu.

Gwamna Bala Mohammed ya taba zama sanata
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

An zabi Bala Mohammed a matsayin Sanata a ranar 21 ga Afrilu, 2007, domin wakiltar al’ummar Bauchi ta Kudu a majalisar dattawa, bayanai daga shafin bauchistate.gov.ng sun tabbatar da hakan.

Ya rike wannan mukami a majalisar dattawa har zuwa lokacin da aka nada shi Ministan babban birnin tarayya Abuja a watan Afrilun 2010.

Gwamna Bala Mohammed ya lashe zaben gwamnan Bauch a ranar Litinin, 25 ga Maris, 2019 a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Hakazalika, Gwamna Bala Mohammed ya sake lashe zabe karo na biyu a shekarar 2023.

INEC ta ce Bala Mohammed ya samu kuri’u 525,280, yayin da babban abokin hamayyarsa, Sadique Abubakar na APC, ya samu 432,272.

2. Uba Sani (jihar Kaduna)

Gwamna Uba Sani ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa bayan ya lashe zabe a shekarar 2019.

Kara karanta wannan

Yunkurin juyin mulki: Sojojin Najeriya 16 za su fuskanci hukuncin kisa

Gwamna Uba Sani ya yi nasarar lashe zaben gwamnan Kaduna
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna na jawabi a wajen taro Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Uba Sani wanda ya yi takara a inuwar APC ya kayar da sanata mai ci a wancan lokacin, Shehu Sani na jam'iyyar PRP, sai Lawal Adamu ya rike tutar PDP.

A shekarar 2023, Uba Sani ya samu nasarar lashe zaben gwamnan jihar Kaduna a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, tashar Channels tv ta kawo rahoton.

A sakamakon da INEC ta sanar, Uba Sani ya samu kuri'u 730,002 yayin da babban abokin hamayyarsa, Isah Ashiru Kudan na PDP, ya samu kuri'u 719,196.

3. Hope Uzodinma (jihar Imo)

An fara zabar Hope Uzodinma a matsayin sanata mai wakiltar Imo ta Yamma a majalisar dattawa a shekarar 2011, sannan aka sake zabarsa a 2015.

Jaridar Vanguard ta ce a ranar 14 ga Janairu, 2020, an ayyana Sanata Hope Uzodinma a matsayin gwamnan jihar Imo sakamakon wata nasararsa bayan zabe.

Babban alkalin alkalan Najeriya (CJN), Tanko Mohammed, ne ya jagoranci alkalan Kotun Koli su bakwai da suka soke nasarar Emeka Ihedioha, tare da ayyana Uzodinma a matsayin gwamna.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bankado masana'antar kera bindigogi, an cafke makeri

A watan Nuwamban shekarar 2023, Gwamna Hope Uzodinma ya sake lashe zaben gwamnan Imo a karo na biyu.

4. Bassey Otu (jihar Cross Rivers)

A shekarar 2011, Prince Bassey Edet Otu ya shiga majalisar dattawa, inda aka zabe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Cross River ta Kudu.

Gwamna Bassey Otu na mulkin jihar Cross Rivers
Gwamna Bassey Otu na jihar Cross Rivers a ofis Hoto: Governor Bassey Otu
Source: Facebook

Hakazalika, a shekarar 2023, an zabi Prince Bassey Otu a matsayin Gwamnan Jihar Cross River a karkashin jam’iyyar APC, tare da mataimakinsa, Rt. Hon. Peter Odey.

Gwamna Bassey Otu ya kama rantsuwar aiki a ranar 29 ga Mayun, 2023, domin jagorantar mutanen jihar Cross Rivera.

5. Ademola Adeleke (jihar Osun)

Ademola Adeleke shi ne sanatan da ya wakilci Osun ta Yamma daga 2017 zuwa 2019 wato ya gaji danuwansa Marigayi Isaka Adeleke.

Ya tsaya takarar gwamnan jihar Osun a zaben 2022 a karkashin jam’iyyar PDP, inda ya kayar da gwamna mai ci a lokacin, Adegboyega Isiaka Oyetola na APC.

Kara karanta wannan

An gano jiha 1 da Tinubu zai iya amincewa a kirkira a Najeriya

6. Douye Diri (jihar Bayelsa)

Douye Diri ya kasance dan majalisar wakilai daga 2015 zuwa 2019, inda ya wakilci Yenagoa/Kolokuma/Opokuma a jihar Bayelsa.

A zaben 2019, an zabe shi Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Tsakiya a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Gwamna Douye Diri ya koma jam'iyyar APC
Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, zaune a ofis Hoto: Douye Diri
Source: Facebook

Douye Diri ya yi takarar gwamnan jihar Bayelsa a zaben shekarar 2019, amma ya yi rashin nasara a hannun David Lyon na APC.

Daga baya, Kotun Koli da ke Abuja ta soke nasarar David Lyon, tare da ayyana Douye Diri na PDP a matsayin gwamna, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Gwamna Diri ya sake nasarar lashe zaben gwamnan Bayelsa a watan Nuwamban 2023, inda ya kayar da Timpre Sylva na jam'iyyar APC.

7. Monday Okpebholo (jihar Edo)

Sanata Monday Okpebholo ya wakilci mazabar Edo ta Tsakiya a majalisar dattawa.

A watan satumban 2023, Monday Okpebholo ya samu nasarar lashe zaben gwamnan jihar Edo karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Sanata Monday Okpebholo ya lashe zaben gwamnan Edo
Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo Hoto: HE Sen Monday Okpebholo
Source: Facebook

Sanata Monday Okpebholo ya kayar da Asue Ighodalo na jam'iyyar PDP mai mulki a jihar a wancan lokacin.

Kara karanta wannan

Bayan 'dan Kwankwaso, wasu karin kwamishinoni sun fice daga gwamnatin Abba

Jaridar Premium Times ta ce Okpebholo ya samu kuri’u 291,667, yayin da Asue Ighodalo ya samu 247,274.

Gwamna Abba Kabir ya koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai rike da mulkin Najeriya.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC ne bayan ya yi murabus daga NNPP wadda ya lashe zabe karkashinta a shekarar 2023.

Abba ya jaddada cewa dalilin komawarsa APC shi ne domin samar da kyakkyawar dangantaka da hadin kai tsakanin Kano da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng