Jigo a PDP Ya Kawo Karshen Takun Saka da Akpabio, Ya Koma Jam'iyyar APC
- Tsohon mai ba PDP shawara kan harkokin shari'a na kasa, Emmanuel Enoidem, ya kawo karshen rikicinsa da Godswill Akpabio
- Sanata Godswill Akpabio ya amshi tsohon kwamishinan hannu bibbiyu lokacin da suka kawo ziyara gidansa tare da gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno
- A yayin ziyarar, an sanar da shugaban majalisar dattawan cewa Emmanuel Enoidem ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Akwa Ibom - Tsohon mai ba PDP shawara kan harkokin shari'a na kasa Barista Emmanuel Enoidem, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a jihar Akwa Ibom.
Enoidem ya gode wa Gwamnan jihar, Umo Eno, bisa rawar da ya taka wajen sasanta shi da tsohon jagoransa na siyasa kuma Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Source: Facebook
Wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa ga shugaban majalisar dattawa, Anietie Ekong, ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a, 23 ga watan Janairun 2026.
Sanarwar ta nakalto Akpabio yana cewa duk wani yunƙuri na hana rikici da karfafa zaman lafiya yana da amfani kuma zai amfanar da jihar.
Akpabio ya yabi gwamnan Akwa Ibom
Akpabio ya yaba wa Gwamna Eno kan abin da ya kira ƙarfafa haɗin kan siyasa a Akwa Ibom, yana mai cewa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin ‘yan siyasa zai taimaka matuƙa wajen hanzarta ci gaban jihar.
Shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne lokacin da gwamnan ya jagoranci wata babbar tawagar shugabannin siyasa domin sanar da shi a hukumance game da matakin Enoidem na shiga APC.
Enoidem ya sansanta da Akpabio
Enoidem ya yi aiki na tsawon shekaru takwas a matsayin kwamishina a zamanin mulkin Akpabio a matsayin gwamnan Akwa Ibom, sannan daga bisani ya zama mai ba PDP shawara kan harkokin shari'a na kasa.
A zaɓen da ya gabata, ya tsaya takara da Akpabio a zaɓen Sanata na Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.
Yayin da yake karɓar tawagar a gidansa da ke Uyo, Akpabio ya ce haɗin kai da zaman lafiya su ne ginshiƙan ci gaban jihar, yana mai jaddada cewa harkar siyasa ta wuce takaddamar zaɓe kaɗai.
A nasa jawabin, Gwamna Eno ya ce tawagar ta zo ne domin sanar da Akpabio game da matakin Enoidem na komawa APC, yana mai bayyana hakan a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa haɗin gwiwar siyasa a jihar Akwa Ibom.
Ya kara da cewa manyan masu ruwa da tsaki a jihar sun yanke shawarar mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya tare da yin aiki tare domin samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba.

Source: Facebook
Tsohon jigo a PDP ya koma APC
A nasa ɓangaren, Enoidem ya bayyana Gwamna Eno a matsayin jagoran haɗin kai, tare da nuna godiya bisa rawar da ya taka wajen sasanta shi da Akpabio.
Ya ce duk da bambancin ra’ayin siyasa da suka taɓa samu a baya, Akpabio har yanzu shi ne jagoransa, kuma ya bayyana shirinsa na yin aiki tare da shi.
Ana sa ran za a karɓi Enoidem a hukumance cikin jam’iyyar APC a wani taron gangami da za a gudanar a Utu Etim Ekpo, ƙaramar hukumar Etim Ekpo, a ranar Juma’a, 23 ga Janairun 2026.
Gwamna Makinde zai ci gaba da zama a PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya kawo karshen jita-jita kan batun ficewa daga jam'iyyar PDP.
Gwamna Makinde ya bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa a cikin jam'iyyar PDP wadda ya lashe zaben gwamna har sau biyu a karkashinta.
Makinde wanda ake hasashen yana burin takarar shugaban kasa a zaben 2027, ya ce ba zai koma APC ko wata jam'iyya daban ba.
Asali: Legit.ng


