Badakalar Fansho: AbdulRasheed Maina Ya Shaki Iskar 'Yanci bayan Shekaru 8 a Garkame
- Abdulrasheed Maina, tsohon Shugaban kwamiti gyara fansho ya fito daga gidan gyaran hali na Kuje
- Kotun Tarayya da kotun daukaka kara sun same shi da laifi kan badakalar kudin fansho sama da N2m
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ce ta gurganar da shi a gaban kotu kan zargin handame kudin ma'aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin gyaran tsarin fansho da aka rushe, wato PRTT, ya samu ‘yanci daga gidan yari.
An tsare Maina a cibiyar gyaran hali ta Kuje da ke Abuja, babban birnin tarayya, inda yake zaman hukuncin daurin shekaru takwas.

Source: Facebook
Wata majiya ta sanar da jaridar The Cable cewa duk da cewa ba a bayyana ainihin ranar da aka sake shi ba, Maina ya fita daga gidan yari a makonni da suka gabata.
AbdulRasheed Maina ya bar kurkukun Kuje
Rahoton ya ce sakin Maina ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, musamman ma ganin irin laifuffukan da aka same shi da su da kuma yadda aka dade ana bibiyar shari’arsa.
Wasu na ganin cewa bai kamata a sake shi cikin shiru ba, yayin da wasu ke tambayar ko an bi dukkannin ka’idojin doka kafin a ba shi ‘yanci.
Har yanzu hukumomin da abin ya shafa ba su fitar da cikakken bayani kan yadda aka aiwatar da sakin ba.
Yadda aka yi shari'ar AbdulRasheed Maina
A watan Nuwamba na shekarar 2021, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta same Maina da laifuffuka da suka shafi almundahana.

Source: Twitter
Adadin kudin da ake zarginsa da handama ya haura N2bn. Hukumar EFCC ce ta gurfanar da shi a gaban kotu a watan Oktoban 2019, bisa tuhume-tuhume guda goma sha biyu.
A hukuncin da ya yanke, alkalin shari’a Okon Abang ya bayyana cewa Maina ya saci kudin fanshon tsofaffin ma’aikata, da dama daga cikinsu sun rasu ba tare da sun amfana da gumin aikinsu ba.
Alkalin ya kuma bayyana cewa Maina ya boye ainihin kansa wajen bude asusun banki biyu ta hanyar amfani da sunayen ‘yan uwansa ba tare da saninsu ba.
Kotun ta same shi da laifi a dukkannin tuhume-tuhumen, tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 61, wanda aka umarci ya gudana a lokaci guda, ya fara aiki daga ranar 25 ga Oktoba 2019.
Maina ya daukaka kara kan hukuncin, amma a watan Mayun 2023 kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru takwas.
Wasu bankuna sun taimakawa AbulRasheed Maina
A baya, mun wallafa cewa Abdulrasheed Maina, ya samu hukuncin zaman gidan yari bayan kotu ta same shi da laifin satar kudin fansho da suka kai sama da N2bn.
Wani rahotonni da aka wallafa a ranar Laraba, 10 ga watan Nuwamba, 2021, ya bayyana cewa wasu bankuna sun taka rawa wajen yadda aka sace kudin fanshon.
Rahoton ya nuna cewa an gudanar da barnar ne ta asusun banki da aka bude a sunayen wasu mutane, lamarin da ya nuna gazawar tsarin sa ido na bankunan da abin ya shafa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

