Lokaci Ya Yi: Matashi Ya Rasu yayin Atisayen Aikin Soja a Kaduna
- Gwamnatin Gombe ta tabbatar da mutuwar wani matashi da ke neman aikin soja yayin atisaye a sansanin Zaria
- An ce marigayin da ya rasu ɗan Gombe ne wanda ya rasa ransa bayan gajerar jinya a yayin horaswar Sojojin Najeriya
- Gwamnatin jihar ta miƙa ta’aziyya, tana roƙon Allah ya gafarta masa kuma ya saka masa da Aljannar Firdausi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Gwamnatin Jihar Gombe ta tabbatar da rasuwar wani matashi a jihar Kaduna da ke karbar horon aikin soja.
Marigayin mai suna Ibrahim Nazifi ya rasu yayin atisaye a sansanin horaswa na Sojojin Najeriya da ke Zaria a jihar Kaduna.

Source: Facebook
Matashi ya mutu yayin atisayen soja a Kaduna
Hakan na cikin wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan Harkokin Tsaro da Hulɗar Gwamnati, Ambasada Yusuf Danbayo, cewar Punch.
Marigayin yana cikin rukuni na farko na matasan da suka yi nasarar shiga aikin soja daga Jihar Gombe, ƙarƙashin shirin 'Nigerian Army Regular Recruit Intake' (NA RRI 90).
Yusuf Danbayo ya ce Ibrahim Nazifi ya rasu ne bayan ya yi gajerar jinya a sansanin horaswar da ake ci gaba da yi.
Gwamnatin Gombe ta bayyana cewa marigayin ɗan asalin ƙauyen Buba Bani ne da ke Kashere a ƙaramar hukumar Akko, tare da lambar neman aikin soja 90RRI-GO-9017726.
Ya ce:
“Cikin matuƙar baƙin ciki da kaskantar da kai ga ƙaddarar Allah Maɗaukaki, nake sanar da rasuwar Ibrahim Nazifi, ɗaya daga cikin matasanmu masu cike da buri da ke samun horaswa a sansanin Sojojin Najeriya da ke Zariya.”

Source: Facebook
Gwamnatin Gombe ta yi ta'aziyyar mutuwar matashin
Danbayo ya bayyana marigayin a matsayin matashi mai kishin ƙasa wanda ya amsa kiran hidimtawa Najeriya, yana mai cewa rasuwar tasa ta girgiza iyalinsa, gwamnatin Jihar Gombe, al’ummar ƙaramar hukumar Akko da ma jihar baki ɗaya.
Ya miƙa ta’aziyyar gwamnatin jihar ga iyalan mamacin, ‘yan uwa, abokai da takwarorinsa, yana roƙon Allah ya gafarta masa kura-kuransa.
“Wannan babban rashi ba iyalinsa kaɗai ya shafa ba, har da daukacin al’ummar Jihar Gombe da masu yi masa fatan alheri.
“Muna roƙon Allah Maɗaukaki ya gafarta masa, ya karɓi kyawawan manufofinsa da ƙoƙarinsa a matsayin ibada, kuma ya saka masa da Aljannar Firdausi.”
- In ji Danbayo
Danbayo ya ƙara da cewa wannan lamari tuna ce ga kowa cewa rayuwa ba ta dawwama, domin kowane rai sai ya ɗanɗana mutuwa, kuma ga Allah ne komawar ƙarshe take.
Sojoji sun musanta tilasta wa matasa aikin soja
A baya, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta fitar da sanarwa, domin wayar da kan al'umma kan jita-jitar cewa za ta tilasta wa matasa shiga aikin soja a kasar.
An danganta jita-jitar da cewa Laftanar-janar Waidi Shuaibu ne ya yi ikirarin tilasta matasa shiga soja, sai dai rundunar ta fito ta karyata rahoton.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta jawo martani daga jama’a, inda wasu suka nemi sojoji su maida hankali kan matsalolin tsaro da ya addabi mutane.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

