Kisan Fatima da Yaranta 6 da Wasu Kashe Kashe 5 da Suka Ja Hankali a Kano

Kisan Fatima da Yaranta 6 da Wasu Kashe Kashe 5 da Suka Ja Hankali a Kano

Kano ta shiga jimami bayan kisan iyalin Malam Haruna Bashir da aka yi da tsakar rana wanda ya tayar da hankali a jihar da ma kasa baki daya.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lamarin kisan gillar da aka yi wa Fatima Abubakar da yaranta shida ya dauki hankalin al'ummar Najeriya wanda ya jawo kiraye-kiraye na daukar mataki.

Yawan kashe-kashe da ake yi a Kano
Kakakin rundunar yan sanda a Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Source: Facebook

Kano: Yawan kashe-kashe da suka dauki hankali

Wannan ba shi ne karon farko ba da ake kisan gilla a Kano wanda ke daga hankali al'umma saboda yanayin yadda ake kisan, cewar BBC Hausa.

Mafi yawan kashe-kashe da suka fi jan hankali su ne wadanda ake shiga har cikin gida a yi ajalin mutane.

Legit Hausa ta duba kisan gilla da suka fi jan hankali a Kano.

Kara karanta wannan

Bidiyon Kwankwaso, Gawuna yayin ziyara ga Haruna Bashir da aka hallaka iyalinsa

1. Kisan Fatima, yaranta 6

A ranar 17 ga watan Janairun 2026 wani mai suna Umar ya tabbatar da aikata laifin kisan Fatima Abubakar da yaranta shida a Unguwar Chiranci Ɗorayi.

Rahotanni daga yan sanda sun tabbatar da cewa marigayiyar kanwar mahaifin Umar ne wanda ya kasance a matsayin ɗa a gare ta.

Umar ya shiga gidan da tsakar rana inda ya yi ajalin matar da yaranta guda shida wurin yin amfani da makami.

Lamarin ya jawo Allah-wadai daga ko ina inda yan sanda suka fara bincike bayan cafke Umar da wasu da ake zargi.

Yadda aka hallaka Fatima da yaranta 6 a Kano
Iyalan Malam Haruna Bashir kafin iftila'in da ya faru da su. Hoto: Abba Hikima.
Source: Facebook

2. Kisan kishiyoyi 2 a Kano

A ranar 13 ga watan Nuwamba, 2025, wasu da ba a tantance su ba sun kai hari gidan wasu mata biyu masu aure — uwargida da amarya a unguwar Tudun Yola, inda suka kashe su tare da ƙona gawarwakinsu.

Lamarin ya girgiza al’ummar jihar matuƙa, ganin cewa an aikata shi ne da rana tsaka, a lokacin da maigidan ba ya nan kuma babu cunkoson mutane a yankin.

Kara karanta wannan

Binciken makamai: Malami na tsaka mai wuya a hannun hukumar DSS, ya fito ya yi magana

A wata sanarwa da rundunar ’yan sandan jihar ta fitar a lokacin, ta bayyana cewa tana gudanar da bincike domin kamo waɗanda ake zargi da aikata laifin.

’Yan sandan sun kuma bayyana cewa sun gano wayoyin hannu guda biyu da ake zargin mallakin masu aikata laifin ne.

3. Kisan gillar da aka yi wa DPO

A farkon watan Yuli na shekarar 2025, wasu matasa sun mamaye ofishin ’yan sanda da ke ƙaramar hukumar Rano a jihar Kano, inda suka hallaka babban baturen ’yan sandan yankin, CSP Baba Ali.

Lamarin ya biyo bayan zargin da wasu matasan garin suka yi cewa jami’an ’yan sanda na da hannu wajen mutuwar wani matashi da ya mutu a tsare bayan kama shi, cewar Punch.

Kisan ya tayar da hankalin jama’a sosai, musamman ganin yadda bidiyon DPO ɗin ya bazu a kafafen sada zumunta, ana nuna yadda ake dukansa ya mutu.

Matasa sun hallaka babban dan sanda a Kano
Marigayi tsohon DPO a Rano, Baba Ali. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Source: Facebook

4. Matashi ya kona masallata a Kano

A ranar 15 ga watan Mayu, 2024, al’ummar Kano suka farka da wani mummunan al’amari da ba za a manta da shi da wuri ba, bayan da wani matashi ya banka wa masu ibada wuta a cikin masallaci tare da kulle su a lokacin sallar asuba a Gezawa.

Kara karanta wannan

Makwabtan Fatima da aka kashe da yaranta 6 a Kano sun fusata rundunar 'yan sanda

Lamarin ya yi sanadin rasuwar aƙalla mutane 23, inda 15 suka mutu nan take, sauran kuma suka rasu yayin da ake jinya a asibiti, Premium Times ta ruwaito.

Kisan ya girgiza zukatan jama’a tare da haifar da suka daga bangarori daban-daban, ciki har da na cikin jihar da ma waje.

Rahotanni sun nuna cewa matashin, mai shekaru 38, ya aikata laifin ne sakamakon rikici da ya shiga da ɗan uwansa kan rabon gado.

A watan Mayun 2025, babbar kotun shari’ar Musulunci a jihar Kano ta yanke wa mutumin, mai suna Shafiu Abubakar, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe masu ibada a masallaci.

Matashi ya kona masallata a Kano
Taswirar jihar Kano da ake yawan samun gisan gilla. Hoto: Legit.
Source: Original

5. Dan China ya kashe budurwarsa a Kano

Wani dan China ya sokawa budurwarsa mai shekaru 23 wuka inda ta sheka lahira a rukunin gidaje na Janbulo na karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Lamarin ya faru wurin karfe 10 na daren Juma'a 16 ga watan Satumbar 2022 bayan saurayin ya kai wa UmmuKulsum ziyara har gidan iyayenta.

Dan uwan mamaciyar ne ya hana jama'a kaddamarwa da 'dan China hukunci inda ya kwace shi tare da mika shi hannun 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Hukuncin da Sarki Sanusi II ya roki Abba ya yi ga makasa Fatima da 'ya'yanta 6

Dan China ya yi ajalin budurwarsa a Kano
Kakakin yan sanda a Kano, Abdullahi Hauruna Kiyawa. Hoto: Nabil Bello Maihausawa, Abba Hikima.
Source: Facebook

6. Kisan Hanifa ya daga hankalin al'ummar Kano

A ranar 2 ga watan Disamban 2021 ne aka sace Hanifa Abubakar, yarinya mai shekaru biyar a Kano a hanyar dawowa daga makarantar Islamiyya, inda ta shafe lokaci ana nema ba a gano inda take ba.

Bayan dogon bincike cikin tsanaki na jami'an 'yan sandan Najeriya, an gano cewa, malaminta kuma mai makarantar da take karatu ne ya sace ta domin karbar kudin fansa daga iyayenta.

Rahotanni sun ce, tuni dama malamin mai suna Abdulmalik ya karbi wasu kudade daga iyayen yarinyar, duk da cewa ya riga ya kashe ta.

Bayan shiga hannu, an garzaya da shi kotu, wannan kuma ya kai ga hukuncin da aka yanke masa na kisa ta hanyar rataya.

An daure matashi da ya kashe Hanifa a Kano
Malam Abdulmalik da ya kashe Hanifa yayin zaman kotu. Hoto: Yar Minista.
Source: Facebook

Abba Kabir ya ba Haruna Bashir kujerar Makkah

An ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin biya wa Haruna Bashir, mutumin da aka kaahe matarsa da yaransa kudin aikin Hajji da Umrah.

Kara karanta wannan

Mutanen Dorayi sun fadi ainihin abin da ya faru kan kisan Fatima da yaranta 6 a Kano

Abba ya bayyana haka ne a lokacin da ya je ta'aziyya ga mutumin bisa wannan jarabawa da ya tsinci kansa a ciki a unguwar Dorayi.

Gwamnan ya kuma dauki nauyin auren da Haruna zai yi, tare da ba shi kyautar sabon gida a wata unguwa ta daban a jihar Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.