Babban Limamin Ilorin, Sheikh Saliu Ya Rasu bayan Shekaru 43 Ya Na Jan Sallah
- Babban limamin Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir Saliu ya riga mu gidan gaskiya bayan ya shafe shekaru 43 yana jan mutane Sallah
- Mai Martaba Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga al'ummar Musulmi
- Za a gudanar da sallar jana'izar marigayi Sheikh Saliu a fadar Sarkin Ilorin da misalin karfe 4:00 na yammacin yau Litinin, 19 ga Janairu, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Al'ummar Musulmi a Najeriya, musamman a masarautar Ilorin dake jihar Kwara, sun wayi gari da labarin rasuwar babban limami, Sheikh Muhammad Bashir Saliu.
Babban sakataren marigayin, Dr. Abdulazeez Arowona, ne ya tabbatar da rasuwar tasa ranar Litinin, 19 ga Janairu, 2026, bayan ya shafe shekaru da dama yana hidimar addini.

Source: Twitter
Sarki ya yi alhinin rasuwar Limamin Ilorin
Sheikh Saliu, wanda aka haifa a shekarar 1950, ya rasu ne yana da shekaru 75, bayan ya kwashe akalla shekaru 43 yana limanci a masarautar Ilorin, in ji rahoton Channels TV.
Mai Martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya nuna tsananin alhini kan wannan rashi, inda ya bayyana limamin a matsayin mutum mai ilimi da hakuri.
Sarkin ya bayyana cewa:
"Rasuwarsa babban rashi ne ga Masarautar Ilorin da daukacin al'ummar Musulmi baki daya, domin ya kasance mai hada kan malamai da jama'a."
Ya kara da cewa:
"Marigayi Imam Saliu ya kasance mutum mai gaskiya, amana da kuma jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin addinai daban-daban."
Tarihin rayuwar limamin da ya rasu
Marigayi Sheikh Saliu shi ne babban limami na 12 a Masarautar Ilorin, inda aka nada shi wannan matsayi a shekarar 1983, lokacin yana da shekaru 33 kacal a duniya.
Sheikh Saliu ya gaji mahaifinsa, Imam Saliu Omo Onida Abdulkadir, wanda shi ne babban limami na 7 a tarihin masarautar dake da tsohon tarihin addinin Musulunci.
A lokacin jagorancinsa, ya kafa cibiyoyin koyar da Larabci da addini da dama, ciki har da 'cibiyar koyar da Larabci da addinin Musulunci ta Imam Saliu' dake Ilorin.

Source: Original
Lokacin jana'izar Babban Limamin Ilorin
An sanar da cewa za a gudanar da sallar jana'izar marigayin a yau Litinin da misalin karfe 4:00 na yamma a fadar Mai Martaba Sarkin Ilorin, in ji rahoton Sahara Reporters.
Daukacin al'ummar garin Ilorin da kewaye sun fara yin dandazo domin halartar sallar jana'izar da kuma yi wa babban malamin addu'ar samun rahamar Ubangiji da gafararsa.
Gwamnan Jihar Kwara da sauran manyan sarakunan kasar nan sun fara aikawa da sakwannin ta'aziya ga iyalan marigayin da kuma Masarautar Ilorin kan wannan babban rashi.
Mai Martaba Sulu-Gambari ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta wa Sheikh Saliu, ya karbi kyawawan ayyukansa, sannan ya sanya shi a cikin gidan Aljannatul Firdausi.
Limami ya rasu yana tsaka da jagorantar Sallah
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani al’amari mai taba zuciya ya auku a kasar Indonesia, inda wani limami ya rasu yana tsaka da sallah tare da mamu a wani masallaci.
A bidiyon da Legit Hausa ta samo, an ga lokacin da limamin ya tada raka’a, har ta kai ga ya yi sujjuda, sujjadar karshe kenan a rayuwarsa.
Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun mika sakon ta’aziyya tare da yi masa addu’ar Allah ya gafarta masa ya kuma sanya aljanna ce makamarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


